Akalla manoma uku ne suka rasa rayukansu da safiyar ranar Juma’a yayin da mutum daya ya ji rauni a kauyen Nkiendonwro da ke gundumar Miango ta Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Madison Davidson, mai magana da yawun kabilar Irigwe ya shaida wa Aminiya cewa, manoman na kan hanyarsu ta zuwa gona yayin da wasu miyagu suka kai musu hari inda suka kashe uku daga cikinsu sannan suka raunata mutum daya.
- Za a dauke ruwan famfo na kwana 5 a Abuja —Hukuma
- Wanda ake tuhuma da kisa ya bukaci alkalin kotun ya daura aurensa
Davidson ya ce an kai wa shugaban ‘yan sandan Bassa rahoton faruwar lamarin.
Ya ce “Yau ma kabilar Irigwe ta sake samun kanta cikin wani tshin hankali.
“Abun bakin ciki wadannan mahara na ci gaba da kashe mu sannan suna mamaye kasar da Ubangiji ya ba mu, amma babu komai mun mika lamarinmu a gareShi.
“Gwamnati da jami’an tsaro ya kamata su tashi tsaye su gudanar da aikinsu yadda ya kamata don kare mutanen kabilar Irigwe,” a cewarsa.
Davidson, ya bayyana sunayen wanda harin ya rutsa da su; Amos David, Ginger Regwe, Abednego Amos da Emmanuel Amos.
Ko da wakilinmu ya tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel kan lamarin, ya ce zai waiwaye shi idan ya samu bayani kan faruwar lamarin.
Ana iya tuna cewa, a ranar 4 ga watan Oktoba ne wasu mutum hudu daga kabilar ta Irigwe sannan wasu uku suka ji rauni, yayin wani hari da aka kai kauyen Hukke.
Fulani makiyaya da kabilar Irigwe sun jima suna jifar juna kan kai hare-hare a tsakaninsu a kauyukan da ke garin Bassa.