✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma 2 sun gurfana gaban kotu kan zargin satar wake

Kotun ta bada belin manoman kan kudi N150,000.

A ranar Juma’a wasu manoma biyu a Jihar Kaduna sun gurfana gaban kotun Majistare da ke zamanta a Kafanchan, kan zargin satar wake a wata gona.

’Ana dai tuhumar mutanen ne da laifin sata da kuma tada zaune tsaye.

  1. Osinbajo zai halarci bikin mika sanda ga Sarkin Kano
  2. ’Yan sanda sun harbe mutum biyu har lahira

Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Dan sanda mai gabatar da kara, Mathias Joseph, ya shaida wa kotun cewar wani mai suna Ishaya Takura daga Kurmun Gwaza ya shigar da kara a hukumar tsaron NSCDC kan zargin mutum biyun da sace masa waken da ya shuka.

Ya kuma ce hukumar ta NSCDC ta gayyaci mutanen amma suka ki bayyana a gabanta.

Joseph ya ce kin bayyanar ya saba da doka sannan ba su nemi zaman lafiya ba.

Ya ce laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 271 da 101 na kundin laifuka na Jihar Kaduna.

Alkalin kotun, mai shari’a Michael Bawa ya bada belin wadanda ake zargin kan kudi N150,000 tare da neman su gabatar da wanda zai tsaya musu.

Daga nan sai ya dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 20 ga watan Yulin 2021. (NAN)