Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga Landa kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hukumomin Saudiyya sun tarbi mutanen a Madina cike da murna da jinjina a gare su.
Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa kungioyin masu tseren kekuna na Madinah da Taibah ne suka tarbi mahajjatan karkashin jagorancin hukumar wasanni ta Saudiyya, inda aka dinga yi musu kade-kade da watsa musu furanni don nuna farin cikin bajintar da suka yi.
Wani jami’i daga kungiyar masu tseren kekuna ta Taibah, Mohammed Al-Sarani, ya shaida wa Saudi Gazette cewa, “Abin da wadannan mahajjata suka yi na zuwa da keke abin a yaba ne.”
An bai wa mahajjatan umarnin su isa har Masallacin Annabi SAW da kekunansu.
Mutanen sun bar birnin Landan ne a ranar 14 ga watan Yuli, inda suka ratsa ta kasashen Faransa da Switzerland da Italiya da Girka da Masar.
Da farko dai sun so ratsawa ne ta kasashen Turkiyya da Syria da Jordan, amma saboda matsalar tsaro sai suka tafi da jirgin ruwa daga Girka zuwa Masar, inda daga can kuma suka shiga jirgin sama da ya kai su Jiddah.
Daga Jiddah ne suka sake hawa kekunansu inda suka je Madina akai karkashin rakiyar motar ‘yan sanda da motocin kungiyar agaji ta Red Cross.
Jagoran matafiyan Abdul Wahid Don White, ya ce, sun shirya tafiyar ce don su nuna wa kasashen da suka ratsa a yayin tafiyar cewa Musuluci addini ne na zaman lafiya da juriya.
Kafin su fara bulaguron nasu dai, mahajjatan wadanda ‘yan wata kungiyar jin kai ce da ke Birtaniya, sun yi fatan hada kudi fam miliyan daya don taimakawa ‘yan Syria da magunguna.