✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maniyyata Aikin Hajji sun yi zanga-zanga kan ninka kudin kujera

Maniyyatan sun roki gwamnati ta sa baki kan karin kudin

Wasu maniyyata Aikin Hajji daga Jihar Legas sun gudanar da zanga-zanga a gidan Gwamnatin Jihar kan ninka kudin kujera a bana.

Maniyyatan sun ce sun riga sun biya kudinsu na hajjin 2020 tun a shekara ta 2019, amma annobar COVID-19 ta hana su tafiya.

Kazalika, sun ce sun ji bakin cikin ganin sako daga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) cewa an samu karin Naira miliyan daya da dubu dari uku kari a kan kudin da suka biya a 2019.

Daya daga cikin maniyyatan da ya kira kansa da wakilin maniyyatan daga dukkan Kananan Hukumomin Jihar ya ce, “Sati uku da suka gabata Kwamishina ya gayyace mu tsohuwar sakateriya ya ce za a kara kudin Aikin Hajji, amma karin ba yawa.

“Mun biya Naira miliyan daya da dubu dari uku, sai muka ga sako daga gwamnati cewa za mu ciko wasu Naira miliyan daya da dubu dari ukun, kuma an bamu wa’adin kwanaki biyar domin yin hakan,” inji shi.

A don haka maniyyatan suka yi kira ga gwamnatin Jihar ta Legas da Kakakin Majalisar Wakilai da su sake duba wannan karin, domin ceto al’ummarsu.