Maniyyata 200 ne suka kammala biyan kuɗin kujera aikin Hajji daga Jihar Taraba.
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware wa jihar kujeru 1,400 domin maniyyatan jihar domin sauke farali a bana, amma mutum 200 kacal suka biya.
Wannan shi ne adadi mafi ƙaranci na maniyyatan aikin Hajji daga jihar.
Kakakin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Taraba, Hamza Baba Muri, ya bayyana cewa a bara alhazai 1,007 me suka yi aikin Hajji daga jihar.
Ya ce saboda ƙarancin maniyyatan da suka kammala biyan kudin kujera, hukumar za ta gudanar da gangami a faɗin jihar domin ba wa jama’a ƙwarin gwiwa su biya.
A cewarsa, jami’an hukumar za su karaɗe ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar domin wannan aikin neman ƙarin maniyyata.