✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United za ta yi wa Harry Kane tayi mai gwabi

Dan wasan zai samu karin £100,000 kan kwantiraginsa na yanzu.

Manchester United za ta yi tayin bai wa Harry Kane kwantaragin fam 300,000 duk mako domin ya koma kungiyar a bazara.

Idan har kungiyar ta samu damar daukar kyaftin din na Tottenham, Kane zai zama daya daga cikin masu karbar albashi mafi soka a Manchester United.

Haka shi ma Kane idan ya amince da kwantaragin komawa United, to dan wasan zai samu karin £100,000 kan kwantiraginsa na yanzu.

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Ingila ya ci kwallaye 26 a dukkan gasa da Spurs, amma 24 daga cikinsu a gasar Firimiyar Ingila ya zura su.

Har ila yau, kocin Manchester United, Erik ten Hag na shirin dauko wani sabon dan wasan gaba a lokacin bazara.