✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester United ta raba gari da Juan Mata

Mata ya shafe shekara takwas da Manchester United.

Manchester United ya sanar da cewar dan wasan tsakiyarta na kasar Spain, Juan Mata zai bar kungiyar da zarar kwantaraginsa ya kare a watan Yuni.

Manchester United ta sanar da yin hannun riga wasu daga cikin ‘yan wasanta da suka hada Paul Pogba da Jesse Lingard, yayin da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar da suka hada Nemanja Matic da Edinson Cavani su ma za su bi sahu.

Juan Mata ya buga wa Manchester United wasanni 285, inda ya lashe kofi uku tun bayan zuwansa kungiyar daga Chelsea kan kudi Yuro milyan 43

A karshe Manchester United ta wallafa a shafinta na Intanet cewa “Muna godiya bayan share shekara takwas da United, muna maka fata na gari.”

Manchester na shirin yin garambawul don farfado da kimarta a duniyar wasanni.