Manchester United ta kwashi kashinta a gidan Tottenham wadda ta lallasa ta ci 2-0 karkashin sabon kociyanta, Ange Postecoglou.
Karawar ita ce ta biyu a makon Firimiyar Ingila, inda Erik ten Hag ya ziyarci Tottenham ranar Asabar.
Bayan da suka koma zagaye na biyu, Tottenham ta ci kwallo ta hannun Pape Matar Sarr, sannan Lisandro Martinez ya ci gida.
Kafin Tottenham ta fara cin kwallo, dukkan kungiyoyin sun taka rawar gani kan wadda za ta hada maki a karawar ta hamayya.
Karo biyu Tottenham ta buga kwallo na bugun tirke ta hannun Pedro Porro da wadda ta doki Luke Shaw ta yi waje.
Tun farko Casemiro ya sama damar farke kwallon da ya buga amma, mai tsaron ragar Totttenham ya yi mata gada.
Da wannan sakamakon United za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a karawar mako na uku, ita kuwa Tottenham za ta ziyarci Bournemouth ne.
Tottenham, wadda ta je ta tashi 2-2 a wasan farko a gidan Brentford ta hada maki hudu kenan, ita kuwa United tana da uku, wadda ta ci Wolves 1-0.
Tottenham ta yi wasa biyu ba tare da Harry Kane ba, wanda ya koma taka leda a Bayern Munich.