✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester United ta kammala daukar Sancho daga Dortmund

Dortmund ta sanar da kammala cinikayyar dan wasan.

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da ke kasar Jamus, ta tabbatar da kammala cinikayyar dan wasan gabanta zuwa Manchester United.

Manchester United ta sayi dan wasan akan kudi €85m bayan shafe tsawon lokaci ana ciniki kan kudin da za a saye shi.

  1. Lasisin tuka Adaidata Sahu ya koma N100,000 —KAROTA
  2. Yadda kwacen waya ke zama ajalin jama’a a Najeriya

Dan wasan wanda dan asali kasar Ingila ne, ya dade da nuna sha’awarsa na komawa kungiyar Manchester United.

Bayanai sun ce kungiyar ta shafe tsawon shekara daya tana zawarcinsa, inda a yanzu cikin wannan mako ta kammala cinikayyar.

Dan wasan yanzu haka na tare da tawagar Ingila da ke buga gasa Euro 2020, inda ta je matakin kusa da na karshe a gasar bayan samun nasara a kan kasar Jamus da ci 2-0.