✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester United ta dauki Erik ten Hag a matsayin sabon kocinta

Ten Hag ya rattaba hannu na tsawon shekara hudu a Manchester United.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta dauki kocin Ajax, Erik ten Hag a matsayin sabon kocin da zai horar da ’yan wasanta a kakar wasanni mai zuwa.

Erik ten Hag ya rabbata hannu har zuwa karshen kakar wasanni ta 2025 tare da damar karin wata shekara guda a kan kwantaragin.

Manchester United ta biya Ajax Fam miliyan biyu a matsayin kudin sanya hannun kocin.

Kungiyar ta dauki tsawon lokaci tana tattaunawa da kocin kan yiwuwar sanya mata hannu, don ceto ta daga halin da ta shiga na samun komawa wajen gaza lashe kofi cikin shekara biyar a jere.

Kazalika, Manchester United ta bai wa Ten Hag cikakken ikon gudanarwar kungiyar da kuma sayen ’yan wasan da yake so.

Manchester United ta gaza tabuka abun a zo a gani tun bayan barin kungiyar da Sir Alex Ferguson ya yi, shekara tara da ta wuce.