✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila ta bana

City ta kare kakar ta bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da Liverpool.

Manchester City ta lashe kofin gasar Firimiyar Ingila ta bana bayan ta farke kwallo biyu da Aston Villa ta zira mata a filin wasa na Etihad.

Wannan shi ne dai karo na shida ke nan da kungiyar ta lashe gasar a tarihi.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta kare kakar ta bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da Liverpool, wadda ta doke Wloves 3-1 a wasan karshen da aka fafata a Yammacin Lahadi.

Kwallo biyu da Ikay Gundogan ya ci da kuma wadda Rodri ya zira a cikin minti shida kacal su ne suka bai wa City nasara inda ta lashe wasan da 3-2.

Villa ta shiga gaba a wasan tun farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho.