✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila sau huɗu a jere

Wannan shi ne karo na farko a tarihin Firimiyar Ingila da wata ƙungiya ta lashe gasar sau huɗu a jere.

Manchester City ta lashe Gasar Firimiyar Ingila bayan ta lallasa West Ham da ci 3-1 a wasan ƙarshe na kakar bana da suka fafata a filin wasa na Etihad.

Phil Foden, wadda ya lashe lambar yabon gwarzon ɗan wasar kakar bana ne ya zura kwallaye biyu a mintuna na 2 da na 18.

Sai dai jim kaɗan kafin tafiya hutun rabin lokaci, Mohammed Kudus ya rama wa West Ham kwallo ɗaya a minti na 42 da buga wasan.

Mintuna 14 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci City ta sake ƙara kwallo ɗaya ta hannun ɗan wasan tsakiyarta, Rodri a daidai minti na 59 na wasan.

A wasannin na yau ne da aka fidda zakarar gasar ta bana, bayan an yi tafiya kafada da kafata tsakanin Manchester City da ƙare da maki 91, yayin da Arsenal ta ƙare a matsayi na biyu a teburin gasar da maki 89.

Wannan shi ne karo na farko a tarihin Firimiyar Ingila da wata ƙungiya ta lashe gasar sau huɗu a jere.

Manchester City ta lashe gasar a kakar 2020/2021, 2021/2022, 2022/2023 da 2023/2024, inda a kakar 2022/2023 ta lashe gasar lig lig, FA Cup da gasar Zakarun Turai wato Champions League.