Mai horar da ’yan wasan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce kungiyar ba ta da shirin sayen tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi, a kakar bana.
Tun bayan da dan wasan dan asalin kasar Argentina ya sanar da kawo karshen zamansa a kulob din na Barcelona, duniyar wasanni ta zaku ta ji inda zai sa gaba.
An dai fi hasashen kungiyoyin PSG da Manchester City din a matsayin wadanda zai iya komawa.
Manchester City dai na cikin kungiyoyin da a baya suka nuna sha’awar sayen Messi lokacin da ya taba yunkurin barin Barcelona.
To sai dai a ranar Juma’a Guardiola ya sanar da cewa ba su da aniyar sayen dan wasan.
Ya ce, “Mun kashe makuden kudade wajen sayen Jack Greslish. Zai sa lamba 10 ne saboda mun gamsu da kwarewarsa, kuma muna kyautata zaton Messi zai ci gaba da zama a Barcelona, yanzu gaskiya ma ba ya cikin tunaninmu.”
Guardiola wanda ya horas da Messi a Barcelona a tsakanin shekara 2008 zuwa 2012, ya bayyana takaicin samun labarin kawo karshen zaman da dan wasan ya yi a kungiyar.