Shi kuma kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara tunanin dauke dan kwallon AC Milan na Italiya Aledandre Pato ne inda tuni kulob din ya taya dan kwallon a kan Fam miliyan 10 da dubu 900.  Shi dai Pato ya nuna aniyarsa ta komawa Ingila don cigaba da yin kwallo a can al’amarin da ya janyo hankalin United a kan dan kwallon.  Sai dai kulob din Chelsea da na Stoke City da kuma na Sunderland sun nuna sha’awarsu a kan dan kwallon don haka akwai yiwuwar United ta fafata da su a cinikinsa.  An samu wannan labari ne daga jaridar Daily Telegraph
Manchesrter United ta fara zawarcin Pato
Shi kuma kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara tunanin dauke dan kwallon AC Milan na Italiya Aledandre Pato ne inda tuni kulob…