✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man United ta dauki aron Odion Ighalo

Manchester United ta dauki dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Najeriya Odion Ighalo, daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China a matsayin aro. Babu zabin…

Manchester United ta dauki dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Najeriya Odion Ighalo, daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China a matsayin aro.

Babu zabin sayen dan wasan mai shekara 30 a cikin yarjejeniyar daukar tasa idan ya gama zamansa zuwa karshen kakar bana.

Har yanzu Ighalo, yana China amma ake tsammanin zai isa Ingila a ‘yan kwanaki kadan, ya ci kwallo 39 a wasa 99 a Premier lokacin da ya buga wa Watford wasa a 2014 zuwa 2017.

“Odion kwararren dan wasa ne,” in ji Ole Gunnar Solskjaer.

Rahoton BBC Hausa