✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man fetur ba zai iya rike Najeriya ba – Jakadan Isra’ila

Mukaddashin Jakadan kasar Isra’ila a Najeriya ya ce akwai bukatar kasar nan ta mayar da hankalinta a harkar noma saboda albarkatun man fetur da iskar…

Mukaddashin Jakadan kasar Isra’ila a Najeriya ya ce akwai bukatar kasar nan ta mayar da hankalinta a harkar noma saboda albarkatun man fetur da iskar gas ba za su iya rike kasar nan ba.
Jakada Benny Omer  ya bayyana hakan ne lokacin wani taro kan kimiyya da fasaha ranar Talata a Abuja. Ya ce a halin da ake ciki kusan duka kasashe masu arzikin albarkatun man fetur sun raba kafarsu don inganta tattalin arzikinsu musamman yanzu da farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya.
“Yakamata Najeriya ta bayar da karfi sosai a bangaren noma. Tana da yawan jama’a da filaye da damina mai albarka da hasken rana da kuma duk wani abu da ake bukata a aikin noma,” inji shi.
Ya kara da cewa ya dace hukumomi a kowane mataki su  karfafa aikin noma irin na zamani. Ya ce “Najeriya ta yi sa’ar shugaba wanda yake yaki da cin hanci da gaske. Matsalar cin hanci da rashawa ta kawo cikas ga kyawawan manufofi da dama a kasar nan.”
A karshe ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kashe kudi masu kauri a fannin ilimi da kimiyya da fasaha da kuma aikin noma.