✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mamayar Taliban: Shugaban Afganistan ya ranta a na kare

Taliban ta ce za ta fara ne da magance manyan matsalolin ’yan kasar.

Wani jagora a kungiyar Taliban ta Afghanistan ya ce yanzu za su fara mulki ya ce ka’in da na’in bayan da suka shiga Fadar Shugaban Kasar sakamakon kwace iko da babban birnin kasar na Kabul.

Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda shi ne ya ke jagorantar sashen siyasa na kungiyar ya fada a wani gajeren faifan bidiyo ranar Lahadi cewa za su yasu fara gwajin mulki ne ta hanyar fara magance manyan matsalolin da ke ci wa ’yan kasar tuwo a kwarya.

Wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Aljazeera ya samu ya nuna shugabannin Taliban din kewaye da dakarunsu da ke dauke da makamai suna jawabi da ’yan jarida daga Fadar Shugaban Kasar ranar Lahadi.

Sun shiga fadar ne bayan Shugaban Kasar Ashraf Ghani ya tsere daga kasar ganin yadda suke kara danno kai bayan sun kwace iko da kusan 26 daga cikin 34 na Lardunan kasar cikin kasa da mako biyu.

Sai dai daga bisani, Ghani ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya fice daga kasar ne don kaucewa zubar da jin.

“Taliban ta sami nasarar kwace kasa da takubbansu da kuma bakin bindigu, yanzu sune ke da alhakin kare martaba da darajar kasar da kuma kare mutanenta,” inji Shugaba Ghani.

Dambarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin da Amurka da Kungiyar Kawance ta NATO suka bayar na janye dakarunsu daga kasar ya cika bayan sun shafe kimanin shekara 20 suna fafata yaki.