✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamakon ruwan sama ya sa dalibai rasa jarabawar JAMB a Legas

Dalibai dai sun roki gwamnati da ta tausaya musu

Dalibai da dama ne suka rasa jarabawar share fagen shiga manyan makarantu (JAMB) a Jihar Legas ranar Juma’a bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka.

Rahotanni sun ce ruwan dai ya tilasta wa dalibai da dama rasa jarawabar wacce aka fara ranar Juma’a.

Hukumar dai ta tace cibiyoyi 750 a fadin kasar, inda dalibai kimanin miliyan daya da dubu 700 za su rubuta ta.

A galibin cibiyoyin da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ziyarta, da misalin karfe 7:00 na safe, lokacin da aka fara zangon farko na jarabawar, wakilinmu ya iske dalibai da dama sun isa a makare saboda ruwan.

Lamarin dai ya sa an hana su shiga cibiyoyin zana jarabawar.

A daya daga cikin cibiyoyin da ke Ogba a Jihar, wakilinmu ya iske dalibai da dama na neman taimako saboda an hana su shiga.

A cibiyar jarabawar da ke Wisdom House ma a kan titin Yaya Abatan, ba ta canza zani ba.

Sai dai duk da ruwan saman, wasu daliban da iyayensu suka yi wa rakiya sun iya zuwa cibiyoyin tun wajen misalin karfe 6:00 na safe.

Daliban da suka gaza samun rubuta jarabawar dai sun yi kira ga hukumar da ta duba halin da suka shiga don ta kai musu dauki.

Misis Esther Oladokun, wacce ke zaune a garin Ajunwon na Jihar Ogun na kan iyaka da Jihar ta Legas ta ce saboda la’akari da nisan, ta bar gida tun misalin karfe 5:30 na safe.

Sai dai ta ce abin takaici ruwan saman ya sa ta gaza kai wa wajen jarabawar a kan lokaci, saboda motar da ta shiga ta lalace a hanya.

Ita ma Misis Chiamaka Ezeaputa wacce ta bar gidanta da ke kusa da Jami’ar Bells da ke Otta tun karfe 5:00 na safe ita ma ruwan ya hana ta samun jarabawar.

Ta kuma ce lokacin da ta isa wajen sai aka hana ta shiga dakin zana jarabawar.

Da yake tsokaci a kan halin da daliban suka tsinci kan nasu, Shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya bayyana takaicinsa kan lamarin.

Sai dai ya ce bisa dokokin hukumar, babu abin da za su iya yi ga duk dalibin da ya rasa jarawabar ya zuwa yanzu.