Gwamnatin Mali ta fara bincike kan yunkurin kashe shugaban rikon kwaryar kasar, Kanar Assimi Goita a masallacin idi ranar Babar Sallah.
Mai gabatar da kara, Bourama Kariba Konate, ya ce an kaddamar da binciken ne domin karin haske kan yunkurin caka wa shugaban kasar wuka.
Bayan harin, Kanar Goita ya ce yana cikin koshin lafiya, sannan ya yi watsi da batun.
An dai dauke Kanar Goita da gaggawa, bayan harin a yayin da ’yan sanda suna tsare wasu mutane a Babban Masallacin, inda shugaban kasar ya halarci sallar idin layyar a ranar Talata.
Sau biyu Kanar Goita na jagorantar juyin mulki a cikin kasa da shekara daya a Mali.
Juyin mulkin farko da ya jagoranta shi ne wanda ya hambarar da tsohon Shugaban Kasar, President Ibrahim Keita watan Agustan 2020.
Na biyun kuma shi wanda ya yi wa shugaban rikon kasar, Bah Ndaw a watan Mayun 2021.