Shugbannin Yammacin Afirka sun isa birnin Bamako na kasar Mali domin shawo kan rikicin siyasar kasar bayan sojoji sun yi juyin mulki.
Shugabannin bisa jagorancin tsohon Shuaban Kasa Goodluck Jonathan na kokarin ganin sojojin sun hanzarta mika mulki ga farar hula; musamman wadanda sojojin suka yi wa juyin mulkin.
Bayan tattaunawa da sojojin, tawagar za ta kuma gana da Shugaba Ibrahim Boubacar Ketita da Firaiminista Boubou Cissse wadanda sojojin ke tsare da su.
Yayin da kasashen duniya ke kara matsin lamba ga sojojin, Amurka ta dakatar da bayar da tallafi da kuma horas da dakarun kasar ta Mali.
A ranar Talata ce sojoji masu bore daga sansanin Kati mai makwabtaka da Bamako suka kwace iko daga Mista Keita da Cisse suka tilasta kuma musu yin murabus da rusa gamanti.
Kifar da gwamnatin ta zo ne a lokacin da rikicin siyasar Mali ya kai ga zanga-zangar adawa da neman Shugaba Ketita ya sauka saboda zargin gazawar gwamantinsa.
Gangamain na zargin sa da kasa gamawa da mayaka masu ikirarin jihadi da durkushewar tattalin arzikin kasar da kuma rashawa a gwamnatinsa.
Yanzu dai shugabannin yankin Yammacin Afirkta na kira da a dawo da Shugaba Keita kan mukaminsa, suna masu cewa manufar zuwansu shi ne “tabbatar da dawo da doka da oda nan take” a Mali.