Kasashen Mali da Burkina Faso sun mika wa kungiyar ECOWAS takardar bukatar ficewarsu a hukumance. Ana kyautata zaton Nijar ta bi bayansu kowanne lokaci daga yanzu.
A Lahadin da ta gabata ne gwamnatocin kasashen Mali Nijar da Burkina Faso suka sanar da ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS, bisa zargin kungiyar da yi musu barazana.
Sai dai tun a wancan lokaci ECOWAS ta bayyana cewa ta na dakon wasikun kasashen 3 a hukumance kan bukatar ficewa daga kungiyar.
A cewar ECOWAS yanzu haka ta na aiki tukuru wajen samar da maslaha a kasashen 3 wadanda dukkaninsu ke karkashin mulkin Soji.
- Ana shirin tsige Ganduje daga shugabancin APC
- CAF za ta yi wa Osimhen gwajin shan kwayoyin kara kuzari
Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta aikewa da AFP kwafin wasikar ficewar yayinda Burkina Faso ta shaidawa kamfanin dillancin labaran aikewa da ta ta wasikar.
Karkashin dokokin ECOWAS dai ana bukatar akalla shekara guda wajen aiwatar da wasu shirye-shirye ga duk kasar da ke son ficewa daga cikin kungiyar.
Kasashen na Mali da Burkina Faso da kuma Nijar na matsayin mambobin da aka kafa kungiyar ta ECOWAS da su tun a shekarar 1975 sai dai a baya-bayan nan suna fuskantar takun saka bayan juyin mulkin da Soji a kasashen wanda ya kai ga kakaba musu takunkumai.