✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamin da ake zargi da azabtar da almajirinsa a Kano ya shiga hannu

An kamo malamin ne a garin Nguru na Jihar Yobe

’Yan sanda a Jihar Kano sun kama malamin da ake zargi da azabtar da almajirinsa mai kimanin shekara takwas wanda labarinsa ya karade kafofin sada zumunta na zamani a kwanakin baya.

Dubun malamin, mai suna Ma’aruf Muhammad, mai shekara 24, ta cika ne a garin Nguru na Jihar Yobe.

A kwanakin baya dai labarin almajirin ya karade gari musamman a kafafen sada zumunta na zamani kan yadda ya yi masa rudu-rudu da duka saboda ba ya kawo masa abinci daga wajen bara.

Lamarin dai ya jawo Allah wadai daga bangarorin al’umma daga ciki da wajen Jihar.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kamun a ranar Asabar.

Ya ce Shugaban Hukumar da ke Kula da Hana Bara a Jihar Kanobne ya kai musu rahoton almajirin bayan an tsince shi yana gararamba kusa da wata kwata a unguwar Kofar Mata da ke Kano.

Kiyawa ya ce daga bisani an garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka duba lafiyar shi kafin a sallame shi, inda ya ce an kafa kwamitin da suka shiga farautar malamin daga bisani.

Kakakin ya ce, “Sakamakon binciken farko-farko, wanda ake zargin ya ce shi dan asalin garin Nguru ne da ke Jihar Yobe, inda ya gudo Kano ta jirgin kasa saboda yawan dukan da yake sha a hannun malamin su shi ma.

“Bayan tsananta bincike, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, inda ya ce yana amfani da wayar wuta ta USB ne wajen dukan yaron bayan ya tube masa riga,” inji Kiyawa.

Kakakin ya kuma ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.