✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamin Addini ya bijire wa Sarkin Musulmi, ya gudanar da Sallar Idi a Sakkwato

Ba a yi kowa da’a wurin saba wa Ubangiji.

Wani malamin addinin musulunci mai suna Malam Musa Lukuwa, ya bijire wa umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar a kan tsayuwar watan Shawwal, inda ya gudanar da idin sallah karama tare da mabiyansa a wannan Lahadin.

A Yammacin ranar Asabar ce Sarkin Musulmi ya sanar cewa watan Shawwal na wannan shekara ta 1443 bai kama ba, yana mai cewa kowa ya cika azumi 30 na watan Ramadana sannan kuma sallah Karama ta kama ranar Litinin.

Sai dai tuni malamin da mabiyansa suka gudanar da Idin Karamar Sallar a birnin Sakkwato da karfe takwas na safe na Lahadi.

A bayaninsa ga manema labarai, Malam Lukuwa ya ce ya samu cikakken rahoton ganin jinjirin watan a wasu wurare na Najeriya da wajenta.

Ya kuma ce ba a yi kowa da’a wurin saba wa Ubangiji, “duk wanda ya yi azumi a yau [Lahadi] ya yini ne da yunwar banza ba wanda ya sa shi domin watan azumi ya wuce” a cewarsa.