Atone-Janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya mayar da martani kan zarge-zargen da aka yi masa a ci gaba da binciken da majalisar take yi kan dawo da Abdulrasheed Maina aiki tare da yi masa karin girma.
Aminiya ta gano cewa Malami wanda ya bayyana a gaban kwamitin wanda Sanata Emmanuel Paulker dan jam’iyyar PDP daga jihar Bayelsa ke yi wa jagoranci jiya ya kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa.
Malami ya bayyana a gaban kwamitin da misalin karfe 4 da rabi na yamma sannan majalisar ta yi masa tambayoyi na tsawon awa daya kafin kwamitin ya kyale shi ya tafi bayan ya gabatar da hujjojinsa a gaban kwamitin har sau uku.