✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman sakandare 3 sun rasu a hatsarin mota a Abuja

Hatsarin motar ya yi ajalin malaman uku da ke koyarwa a makaranta daya

Wasu malamai uku da ke koyarwa a wata makarantar sakandare a unguwar Rubochi da ke yankin Kuje a Abuja sun rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan titin Abuja zuwa Lakwaja.

Wani ganau ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 2:15 na yammacin ranar Juma’a a yayin da motar da malaman makarantar suke ciki ta kwace a daidai Gadar Kwaita.

Ya ce motar da ta yi hatsarin kirar Toyota Carina ce mai dauke da lamba 154 KWL, kuma biyu daga cikin malaman sun shige ta ne don a rage musu hanya.

Kwamandan ’yan sanda na yankin, Samuel Ogar Ochi, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar hatsarin, yana mai cewa an mika gawarwakin ga Babban Asibitin Kwali.

Ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da direban ke yi.

Shugaban kungiyar malamai na yankin Rubochi, Tanimu Taru, ya tabbatar da faruwar hatsarin wanda ya ce ya yi sanadin ajalin ’ya’yan kungiyar guda uku.

“Yanzu ina gidan daya daga cikin iyalan mamatan, amma Abubakar Yelwas Yunusa Ladan an birne su tuni tun ranar Juma’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar,” inji shi a lokacin da wakilinmu ya tunutbe shi.

Ya ce tuni iyalan Lazarus Makama suka kammala shirye-shiryen birne shi ranar Litinin.