Malaman makarantun firamare da ke Birnin Tarayya, Abuja, sun shiga yajin aiki a ranar Laraba, kan rashin biyan su wasu hakkokinsu.
Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) Reshen Kubwa da ke Abuja, Kwamared Ameh Baba ya shaida wa Aminiya cewa sun shiga yajin aikin ne bayan cimma matsaya da mambobin kungiyar.
- Kisan Hanifa: Iyaye sun koma zuwa daukar ’ya’yansu daga makarantu kafin lokacin tashi a Kano
- Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci
Ya ce an gaza biyan su wasu hakkokinsu da sauran kudade da suka shafi karin matsayi tun daga shekarar 2011.
Shugaban na NUT, ya ce a baya sun amince su janye yajin aikin da suka shiga a watan Nuwambar 2021, sakamakon shiga lamarin da Sanata Philip Adudah ya yi tsakaninsu da shugabannin makarantun.
“Har yanzu sun gaza cika alkawari, ga dukkan alamu sun mayar da hankali kan harkokin yakin neman zabensu,” a cewar Baba.
A baya Aminiya ta rawaito yadda malaman makarantun Firamaren da ke Abuja suka tafi yajin aiki har sau uku, wanda na karshe da suka tafi sai da suka shafe mako biyu, kafin su janye.