A makon da ya wuce ne wasu malaman addinin musulunci na kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah reshen jihar Oyo, suka amsa goron gayyata da ‘yan uwansu ‘yan darika suka yi musu zuwa wajen bikin saukar karatun Alkur’ani da dalibai 13 maza da mata na makarantar Almadrasatul Ali-Al Sabahiya suka yi, a harabar babban masallacin unguwar Sabo cikin birnin Ibadan.
Liman Ratibi na masallacin Daru Da’awa da ke Sabo Ibadan, Ustaz Mustapha Abdul Malik, shi ne ya jagoranci wasu malamai na kungiyar Izala zuwa wajen wannan saukar karatun Alkur’ani da ‘yan darika suka gayyace su, wacce aka gudanar a gaban Shugabannin al’ummar Hausawa, wadanda suka hada da Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru.
Da yake yi wa wakilinmu bayani dangane da wannan ziyara, Ustaz Mustapha Abdul Malik, ya ce, “a matsayinmu na musulmi, mun halarci wannan wuri da aka gayyace mu zuwa wajen wannan aiki na alheri da ya shafi koyon karatun Alkur’ani da aiki da shi ne, domin mu kara karfafa gwiwar yaranmu su bayar da himma da mayar da hankali a kan koyon karatun Alkur’ani mai girma da fahimtar addinin Musulunci yadda ya kamata.”
Da yake amsa wata tambaya, malamin ya ce, “duk musulmin da ya yi imani da Alkur’ani da sunnar Annabi Muhammad (SAW) ya san cewa, babu abin da zai kawo hadin kan Musulmi da dinke barakar da ke tsakaninsu kamar riko da Alkur’ani da sunnar Annabi Muhammad (SAW). Idan har mutane suka tabbata a kan hakan, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya hada kawunan Sahabbai da musulmin duniya baki daya, to kuwa Allah zai taimaka mana wajen shawo kan matsalar rashin fahimtar juna da guna-guni a tsakaninmu. Kuma, idan Allah ya so, sai wannan ziyara ta mu zuwa wurin karatun Alkur’ani mai girma ta zama sanadin karshen rashin fahimtar juna a tsakaninmu. Saboda haka, ina yin kira ga ‘yan uwa musulmi baki daya mu tashi mu yi karatun neman ilmin addininmu ta cikin Alkur’ani da Hadisan Annabi Muhammad da yin aiki da abubuwan da ke cikinsu. Idan muka yi hakan, to idan Allah ya yarda za mu samu sauki da rahamar Ubangiji a duniya da lahira.”
“Yin hakan zai taimaka wajen kawo karshen rashin fahimtar juna da ake samu a tsakanin musulmi. Mu ma a shirye muke mu halarci wajen taron wa’azi ko saukar karatun Alkur’ani idan ‘yan uwan namu suka gayyace mu,” a cewar babban malamin makarantar Almadrasatul Ali, Ustaz Ibrahim dan’azimi Bako, wanda ya nuna matukar farin ciki da jin dadi ne a kan amsa goron gayyatar da ‘yan uwansu malamai daga kungiyar Izala suka yi,
dalibai mata takwas da maza biyar na wannan makaranta ta Almadrasatul Ali ne suka karanto wasu daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma a gaban taron manyan malaman addinin Musulunci da Dattijan gari da Hakimai da wakilan kungiyoyi daban-daban, inda iyayensu suka sanya musu albarka. Sarkin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru su ne suka mika wa daliban takardun shaida (satifiket) da makarantar ta tanada.