Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Neja, ta ce malaman firamare da daman gaske a makarantun gwamnatin jihar ba su iya karatu ko rubutu ba.
Shugaban Hukumar, Isah Adamu, ya ce a cikin kowadanne dalibai 10 a makarantun firamaren gwamnatin jihar, mutum tara ba su iya karatu da rubutu ba.
- Shekau ya zabi a yi masa azaba a lahira —Shugaban ISWAP
- Zamfarawa ku kare kanku daga ’yan bindiga —Matawalle
“Halin da wasu makarnatun ke ciki abin takaici ne sosai saboda za ka tarar malamai ba sa iya koyarwa yadda ya dace; akwai ma malaman da ba sa iya karatu ko rubutu,” inji shi.
Ya bayyana haka a taron lalubo hanyoyin farfado da ilimin firamare a Jihar.
An kira taron ne da nufin samun goyon bayan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi domin shawo kan kalubalen da ilimin firamaren ke fuskanta a jihar.
A cewarsa, taron na ranar Alhamis, ya zama dole saboda bayan hukumar ta kashe makudan kudade wajen sanya yara 250 a makarantar Suleja Academy, daga bisani an gano babu abin da yaran suka tabuka a harkar karatun.
“Bayan mun samu goyon bayan Gwamna Abubakar Sani Bello mun bai wa kanmu ajandar aiki babu kama hannun yaro domin mu inganta ilimin firamare a Jihar Neja.
“Abun da muka fara yi shi ne zagaya jihar baki daya domin ganin halin da makarantun suke ciki. Abin da muka tarar a kasa babu dadin ji.
“Halin da wasu makarnatun ke ciki abin takaici ne sosai. Za ka tarar malamai ba sa iya bayar da karatu yadda ya dace, sannan mafi munin ma akwai malaman da ba sa iya karatu ko rubutu.
“Domin fahimtar hakikanin lamarin, mun kafa kwamitin da ya binciki harkar koyarwa da gudanarwa a dukkanin kananan hukumomin jihar 25.
“Rahoton kwamitin ya gano cewa da dama daga cikin malaman ba sa iya karatu ko rubutu,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa a jarrabawar shiga makarantun sakandaren tarayya dalibai 21 ne kawai cikin 250 suka ci jarrabawar.
A jawabinsa, gwamnan jihar, Abubakar Bello, ya koka kan lalacewar ilimin firamare a jihar.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Ahmed Ketso, ya wakilta, ya bukaci mahalarta taron da lallai su lalubo hanyoyi masu dorewa na inganta harkar ilimin firamare a jihar.
A watan Mayu, an sallami wadansu malaman firamare a Jihar ta Neja bisa zargin su da amfani da takardun bogi da kuma kin zuwa wajen aiki.