✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malamai sun yi watsi da ka’idojin bude masallatai a Ilori

Majalisar  Malaman Birnin Ilori a jihar Kwara ta yi watsi da ka’idojin da gwamnatin jihar ta sanya na bude masallatai a jihar. Malaman sun bayyana…

Majalisar  Malaman Birnin Ilori a jihar Kwara ta yi watsi da ka’idojin da gwamnatin jihar ta sanya na bude masallatai a jihar.

Malaman sun bayyana ka’idojin gwamnatin a matsayin tsaurara da babu yadda za a iya cika su.

A sanarwar da Sakataren Majalisar Malaman, Mai Shari’a Salihu Olohuntoyin Mohammed (mai murabus) ya fitar, Majalisar ta ce:

“Kayyade shekarun masu halartar Sallar Juma’a zuwa  kasa da 65 abu ne mai wuya, domin a Musulumci limamai su ne jagororin addini, kuma akasarinsu sun haura shekaru 65.

“Mun kuma lura daukacin ka’idojin na da matukar tsauri wadanda zai yi wuya a tursasa jama’a su cika su.

“Don haka muke kira ga gwamnatin da ta ci gaba da rufe masallatan Juma’a har sai ta sake duba a kan ka’idojin”.

A kwanakin baya ne Kwamitin Yaki da Annobar COVID-19 na jihar Kwara ya zayyana ka’idojin da za abi a yunkurin gwamnatin jihar na bude masallatan Juma’a daga ranar Juma’a 5 ga watan Yuni.

Sai Majalisar Malaman ta ce sun yi tsauri matuka duk da cewa tana sane an yi hakan ne domin dakile yaduwar annobar a jihar.