Wata malamar makaranta mai suna Joy Eze, ta yi karar mijinta Nuel Chukwu a gaban wata Kotun Al’adu saboda kaurace wa abincinta.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, matar ta yi karar mijin ne kan zarginta da yake yi na zuba masa guba a abinci.
- An kama matar da ta sheka wa matashi tafasasshen ruwa a Kano
- Kotu ta ba PDP umarnin sake zaben fidda dan takarar Gwamna a Zamfara
Da take gabatar da bukatar neman a tsinka igiyar aurensu a gaban kotun mai zamanta a Unguwar Jikwoyi da ke Abuja, Joy ta ce ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.
Joy wadda ta nemi a raba auren, ta kuma rokin kotun ta ba ta rikon ’ya’yansu.
“Ya daina cin abincina, idan kuma na nemi jin bahasi sai ya ce yana sane da kulle-kullen da nake yi don ganin bayansa.
“Ya riga ya sanar da ’yan uwansa cewa a duk lokacin da ya mutu to alhakin yana wuyana, a cewarta.
Joy ta kuma shaida wa kotun cewa, mijin nata ya sa ’ya’yan da suka haifa sun dora mata karan-tsana.
“Ya bata min suna a wurin yayana saboda irin munanan abubuwan da yake fada musu a kaina.
“Ya sanar da su [’ya’yana] cewa karuwanci nake fita kuma duk kayayyakina da takalma da jakunkuna ’yan dadiro ne suka saya min.”
A nasa martanin, mijin Joy wanda ke sanaar kabu-kabu da babur mai kafa uku, ya musanta zarge-zargen da matar ke yi masa.
Alkalin kotun, Labaran Gusau ya dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Satumba.