✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Makwabcina ya yi wa ’yata cikin shege

Kawun matashin ya ba da kudi a zubar da cikin da ake takaddama a kai

Wani magidanci ya shaida wa Kotun Musulunci da ke zamanta Sabon Garin Zariya, Jihar Kaduna, cewa dan makwabcinsa ne ya yi wa ’yarsa ciki shige ya kuma ba da N15,000 don a zubar da cikin.

Ranar 12 ga watan Disambar 2020 matashin ya shigar da kara a gaban kotu yana neman ta wanke shi daga zargin da budurwar mai shekara 17 da mahaifinta suke masa cewa ya yi mata cikin shege.

Mahaifin yarinyar ya bayyana wa kotun cewa: “’Yata ta fada min cewa shi ne ya yi mata ciki.

“Tun da farko na kai kara kan lamarin a Caji ofis na Kasuwar Mata da ke Sabon Gari, inda ’yan sanda suka kama shi suka tsare shi a wurinsu.

“Dangin wanda ake zargin tare da mai dagacin unguwar Jushin Waje wanda kawunsa ne suka same ni cewa mu sasanta kan batun.

“Suka ba ni N15,000 cewa a zubar da cikin amma na ce musu addinina ya haramta hakan kuma ni ba zan aikata ba,” inji mahaifin budurwar.

Ya kuma bayyana wa kotun cewa ’yar tasa ta haife cikin da ta dauka kuma an samu da na miji.

“Da ta fara nakuda sai na kira kawunna, ya kuma yi alkawarin bayar da N15,000 don a biya kudin magani.

“’Yar tawa ta haifi namiji kuma daga shi wanda ake zargin har danginsa babu ko mutum guda da ya zo ganin dan.

“Bayan kwana uku sai na sa matata ta kai wa dangin wanda ake zargin jaririn, amma da ta kai jaririn sai suka ki karbar sa,” inji shi.

A yayin sauraren karar, alkalin korun Mai Shari’a Shittu Umar, ya tambayi wanda ake tuhuma game da kudin, amma ya musanta ba da kudi don a zubar da cikin, amma ya ce “kawuna ne ya ba shi (mahaifin yariyar) kudin.”

Bayan ya gama sauraren karar, sai Mai Shari’a Umar, ya dage sauraran karar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2021 don ci gaba da sauraron shari’ar.