Wani makusancin tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Tonye Princewill, ya sanar da ficewarsa daga APC saboda tsayar da ’yan takara biyu Musulmai a jam’iyyar.
Dan takarar Shugaban Kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dai ya sanar da sunan tsohon Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben 2023 mai zuwa, duk da kasancewar duka su biyun Musulmai.
- Fari ya kashe dabbobi miliyan daya a Habasha —Rahoto
- ’Yan wasa 10 da ke takarar gwarzon dan kwallon Afirka na 2022
To sai dai Princewill, wanda ya taba neman takarar Gwamnan Jihar Ribas a 2015 karkashin jam’iyyar Labour, ya ce ba zai lamunci matakin jam’iyyar ba saboda rashin adalci ne karara.
Sanarwar ficewar tasa dai na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike zuwa ga Shugaban APC na mazabarsa ta Tahhed Royal da ke Buguma a Karamar Hukumar Asar Toru, dauke da kwanan watan 12 ga watan Yulin 2022.
Ya bayyana rashin jindadinsa da matakin da jam’iyyar ta dauka, inda ya ce ba zai yiwu ya rika da’awar adalci a jiharsa ba, amma kuma ya yi shiru idan aka yi rashin adalcin a matakin kasa.
Pincewill ya ce akwai rashin la’akari daga APC ta tsayar da ’yan takara biyu daga addini daya, duk kuwa da yadda rashin amincewar da shugabannin addini da na siyasa daga sauran bangarorin kasar nan suka nuna.
Wasikar ta ce, “Duka da ina jinjina wa mai gidana, Rotimi Amaechi, kan irin kokarin da yake yi, ba zan iya kare matsayin jam’iyyata ba na tsayar da Musulmai biyu a matsayin ’yan takararta duk da rashin amincewar da wasu suka nuna.
“Wannan wani mummunan abu ake kokarin, wanda sam bai kamata ba, ko da an yi nasara, zai samar da rarraunan shugabanci.
“A irin yanayin da muke ciki, ba ni da wani dalili da hankalina da zan ci gaba da zama a jam’iyyar da ta sadaukar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa ga samun nasararta a zabe,” inji shi.