✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Makullin zaman lafiyar Najeriya na hannun Nnamdi Kanu – IPOB

Kungiyar ta ce dole a sako Kanu ba tare da wani sharadi ba

Kungiyar ’Yan Awaren biyafara ta IPOB ta yi gargadin cewa samun zaman lafiyar Najeriya ko akasin haka na hannun jagoransu, Nnamdi Kanu.

IPOB ta kuma dattawa da ’yan siyasar jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da kada su kuskura su sake shigowa yankin ba tare da Kanu ba.

Mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Kungiyar ta ce, “Yayin da ’yan ta’adda da matsalar tsaro suka tasam ma kwace Babban Birnin Tarayyar Najeriya na Abuja, mu ’yan IPOB, karkashin jagorancin Nnamdi Kanu muna kira ga wadanda ke kiran kansu da dattawan kabilar Ibo da ke Abuja da kada su sake su dawo yankinmu ba tare da Nnamdi Kanu ba.

“Muna murna kan yadda kusan dukkan hasashen da Kanu ya yi suke kokarin tabbata. Muna tsamammanin nan da wani dan lokaci wadannan ’yan ta’addan za su sami damar karbe Aso Rock, sannan su tabbatar da cewa mutanen da suka kakaba kansu a kan shugabancin Najeriya babu su, kamar yadda Kanu ya yi hasashe.

“A bayyane yake a fili cewa da zarar wadannan mutanen sun kwace Abuja za su fado Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabashin Najeriya. Yanzu gaba daya Kudu ba ta tsira ba, kuma ya kamata dukkanmu mu tashi tsaye.

“Saboda haka muke ba dukkan dattawanmu na Abuja shawara da kar su dawo Kudu maso Gabas ba tare da Kanu ba. Ya zama wajibi su yi duk mai yiwuwa su dawo gida tun da dai Abuja yanzu ba kalau take ba.

“Ba za mu kyale su ba muddin suka dawo ba tare da sun tabbatar an sako shi daga hannun DSS ba tare da wani sharadi ba,” inji IPOB.