✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tabbas kan Coutinho; Ighalo zai ‘koma’ China; Icardi zai zauna a PSG

Da alamu kungiyar Barcelona ba ta shirin dawo da dan wasanta Philippe Coutinho da ta tura aro zuwa kungiyar PSG zuwa Camp Nou, ganin cewa…

Da alamu kungiyar Barcelona ba ta shirin dawo da dan wasanta Philippe Coutinho da ta tura aro zuwa kungiyar PSG zuwa Camp Nou, ganin cewa ba’a fara tattauna yiwuwar dawo da shi kuniygar ba.

Wannan dai yana faruwa ne lokacin da kungiyar da Coutinho yake aro Bayern Munich ta yi burus da batun tsawaita kwantiraginsa.

A gefe guda kuma kungiyoyin Frimiya sun fara hangen dauko dan wasan. PSG na shirin bai wa Icardi kwantiragi shi kuma Ighalo yana iya sake komawa China, ko meyasa?

Zamu kori duk ma’aikacin da ya fitar da bayanai ba bisa ka’ida ba — Gwamnati

Almajiri Dan Nijar na cikin wadanda jihar Kano ta mayar Kebbi

 

— Makomar Coutinho tana kasa tana dabo

Makomar dan wasan tsakiya da Kungiyar Barcelona ta sayo daga Liverpool ta tura zuwa Bayern Munich aro, Philippe Coutinho ta shiga halin rashin tabbas.

Jaridar Skysport ta bayyana cewa zaiyi wuya Coutinho wanda yake kokarin murmurewa daga rauni ya sake takawa Bayern Munich leda saboda kin sabunta kwantiragin aronsa da suka yi da kuma zawarcinsa da kungiyoyin frimiya suke yi.

 

— Kwantiragin dan aron dan wasan zai kare 30 ga watan Yuni.

Ana dai sa ran cikin sati biyu masu zuwa zai gama murmurewa har ma ya dawo taka leda a sauran wasanni hudu da kungiyar take da su kafin karkare kakar bana.

Amma hukumomi a kungiyar ba su nuna yiwuwar damawa dashi a nan gaba ba.

Kungiyoyin Frimiya da suka hada da Chelsea, Arsenal da Tottenham tuni suka fara zawarcin dan wasan mai shekara 27 wanda ya sauya sheka daga kungiyar Liverpool a kan euro 145 shekaru biyu da suka gabata.

Har yanzu Coutinho yana da sauran shekaru uku a kwantiraginsa da Barcelona.

 

— PSG na shirin tabbatar da Icardi

Dan wasan gaba na kungiyar Inter Milan wanda yake aro a kungiyar PSG, Mauro Icardi na shirin zama daram a kungiyar bayan PSG din ta dauki aniyar sayo shi daga Inter din.

Jaridar ESPN ta rawaito cewa tuni aka fara tattaunawa da wakilin dan wasan a kan lamarin.

Dan shekara 27, Icardi ya koma taka leda a Faransa ne a kakar bara wanda kuma kungiyar take da daman sayo shi a kan farashin Euro miliyan 70.

A halin yanzu dai Daraktan Wasanni na Kungiyar PSG, Leonardo yana bukatar kungiyar Inter Milan da ta sassauta farashin dan wasan ganin halin da kungiyar ta shiga dalilin annobar coronavirus.

A farkon kakar da ya taka leda a PSG, Icardi din ya ci kwallaye 21 duk da cewa ya samu rauni da ya hana shi wasa tun watan Disamba har Fabrairu.

 

— Ighalo Ighalo zai koma China

Dan wasan gaba da Manchester United ta dauko aro daga kungiyar Shanghai Shenhua na shirin sake komawa kasar ta China saboda gaza cimma matsayar tsawaita kwantiraginsa da kungiyoyin biyu suka yi.

Kwantiragin aron zai kare ne a ranar 31 ga watan Mayu.

United ta dauko Ighalo mai shekaru 30 a watan Janairu domin cike gurbin da rashin Marcus Rashford ya samar yayin da ya samu rauni.

Tasirinda cutar coronavirus ta yi a kan wasanni ya sa kwantiraginsa zai kare ba tare da tsawaita shi ba wanda ake sa ran Rashford din zai dawo buga wasa kafmin gasar Frimiya ta dawo a watan Yuni.

Kocin kungiyar ta United Ole Gunnar Solskjaer yana fatan tsawaita kwantiragin aron na Ighalo ganin cewa kungiyar tana ci gaba da taka leda a gasanni uku wanda hakan yake nufin za ta iya buga wasanni 18 a cikin watanni biyu.

Tun zuwansa United, Ighalo ya ci kwallaye hudu a wasanni takwas da ya buga.