✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mako 2 da Buhari ya bai wa Ministan Ilimi ba zai yi aiki ba idan… — ASUU

Buhari ya bai wa ministan ilimi wa'adin mako biyu ya kawo karshen yajin aikin.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta ce wa’adin mako biyu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, na kawo karshen yajin aikin da suke yi, ba zai yi tasiri ba idan har aka sanya Ministan Kwadago Chris Ngige, a cikin sulhun.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Talata ne Buhari ya umarci Adamu da ya warware matsalar yajin aikin da ASUU ta tsunduma na wata da watanni ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai da yake mayar da martani kan wannan umarni a lokacin da yake amsa tambayoyi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya jaddada cewa Ngige a matsayinsa na “Babban Mai Sasantawa” shi ne babban jigon da ke rura wutar rikicin da ake samu a manyan makarantu a fadin kasar nan.

Osodeke ya ce, “To, muna addu’ar wannan wa’adin ya yi aiki a wannan karon domin idan za ku tuna, a baya an ba da irin wannan umarni, inda NIREC karkashin jagorancin Sarkin Musulmi da Kungiyar Kiristoci ta CAN suka shiga tsakani. Amma wane sakamako aka samu?”

Kungiyar ASUU ta fara yajin aikin gargadi na tsawon wata guda a ranar 14 ga watan Fabrairu, sai dai sauran kungiyoyi sun zargin Gwamnatin Tarayya da gaza biyan bukatunsu.

Lamarin yajin aikin ASUU abu ne da ya tsaya wa mutane da dama a rai, musamman iyaye da dalibai da masu gudanar da harkokin neman abinci a dalilin harkokin manyan makarantu.