A daidai lokacin da ake daura auren Hanan, diyar Shugaba Muhammadu Buhari, ranar Juma’a, akwai matasan da suka suka fada cikin mummunan yanayi saboda an kayar da su.
Da ba don ya ce ya rungumi kaddara ba, da an lissafa Abdullahi Bashir, wani makiyayi mai shekara 22 dan Jihar Adamawa, a jerin wadannan matasa.
- Wani matashi ya yi yunkurin kashe kansa kan auren Hanan Buhari
- Kayatattun hotunan bikin Hanan Buhari
Shi dai Abdullahi ya kasance ba shi da wani buri a rayuwarsa fiye da auren Hanan, ya kuma yi iya kokarinsa domin kulla soyayya da ita, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Da kokarinsa na haduwa da ita ya bayyana mata kaunarsa ya ci tura, sai Bafulatanin ya shiga kafafen sada zumunta ya wallafa bidiyonsa yana alkawarin ba da shanu 150 a matsayin sadaki idan har Hanan ta yarda ta aure shi.
Bayan samun labarin matsowar aurenta da wani, matashin ya sanar cewa zai bayar da gudunmuwar shanu 50 domin bikin, kuma ya rungumi kaddara.
Kimar shanu 150
“Zan ba da shanu 150 a matsayin sadakin Hanan ne ba wai don in nuna ni mai kudi ba ne; gaskiya ni ba kowa ba ne.
“Ba darajar kudin shanu a kasuwa nake dubawa ba, abin da nake dubawa shi ne kimar shanu a wurin Bafulatani.
“A wurin Bafulatani gara ya ba ka Naira miliyan 1 da ya ba ka sa daya.
“Hakan shi ke nuna muhimmancinta a gare ni da yadda nake kaunar ta”, inji shi.
Abdullahi ba Bafulatani mai yawo da sanda yana kiwo ba ne kawai.
Yana da shaidar kwarewa a harkar intanet daga Google; mutum ne mai matukar sha’awar daukar hotuna da bidiyo da kuma fasahar kasuwancin zamani ta intanet.
“Ni ne na bude nake kuma kula da shafin intanet na Koode Radio International, wani gidan rediyo na harshen Fillanci a Abuja.
“Kuma ni dan jarida ne a matsayin wakili mai aikin wucin gadi”, kamar yadda ya shaida wa Aminiya a cikin wata hira ta musamman.
A cewarsa, yanzu ya koma amfani da shafinsa na YouTube domin wayar da kan ’yan uwansa Fulani a kan dabarun kiwo na zamani da kuma horar ta matasa a kan fasaha da kirkire-kirkire.
Kaunar daukar hoto
Ya ce Hanan ta fara daukar hankalinsa ne bayan ya ga hotunanta a shafukan sada zumunta tana daukar hoto a wajen wani taro a Bauchi.
Ba a fiye samun mace ’yar Arewacin Najeriya na aikin daukar hoto ba, ballantana ma a ce budurwa Bahaushiya ko Bafulatana.
A yayin karanta bayananta a shafukanta na sada zumunta ya ga wasu hotuna da sakonni da ke nuna yadda shi da ita suka yi tarayya, duk da cewa bai taba ganin ta ba: ita ma tana son daukar hoto.
Kafin ka ce kwabo har abokansa na kusa sun san yadda ya kamu da son budurwar da bai taba haduwa da ita ba, har suka sa masa suna Gorko Hanan, wato mijin Hanan da Fillanci.
Ana haka ne daga baya ya gano cewa mai daukar hoton da ta sace masa zuciyar diyar Shugaba Buhari ce.
Maimakon ya ja da baya, sai ya ci gaba da bincike da neman karin bayani a kan matashiyar, bai kuma karaya ba.
Makantar tunani
Ya ce bai taba lura da cewa ya kamu da son Hanan ba sai da wani abokinsa ya jawo hankalinsa.
“Sai daga baya na san cewa diyar Shugaban Kasa ce”, inji shi.
Ya ce a lokacin ne ya fahimci cewa akwai jan aiki a gabansa.
Duk da haka bai hakura ba, ya kuma dage da kokarin haduwa da ita a duk inda zai iya.
Ya ce saukin kanta da ya gani a yadda ta yarda ta yi aikin daukar hoto ya burge shi.
“Ko a Turai ba kasafai ake ganin ’yar Shugaban Kasa na sana’ar daukar hoto ba”, inji matashin.
Ya gano cewa ya riga ya fada
Ya kasance kodayaushe maganar Hanan yake yi, yana bai wa abokansa labarin kyan halinta da yadda ta jajirce a sana’arta duk da matsayinta.
“Ina yawan yi wa abokaina maganarta ina nuna musu hotunanta. Wata rana wani abokina, Ahmad Faisal, ya tambaye ni ko son ta nake yi?
“Wallahi, a nan ne na gane cewa da gaske son ta nake yi”.
A yunkurinsa na cimma burinsa na auren Hanan, matashin ya nemi goyon bayan wasu fitattun shugabannin Fulani, ya kuma yi takakkiya daga Yola zuwa Abuja ko zai yi sa’ar ganinta.
Yana tunanin a matsayinta na mai saukin kai, Hanan za ta kasance a wurin wani taro a daya daga cikin unguwannin Abuja, tana yin abin da ta fi so, daukar hoto.
Yana kyautata zaton zai iya haduwa da ita.
In da rai da rabo
A tsawon zamansa a Abuja, duk inda Abdullahi ya ji labarin biki da taron manyan mutane sai ya yi maza ya je.
Yana tunanin zai iya ganin Hanan a wurin tana daukar hoto ko a matsayin bakuwa. Amma kuma bai gan ta ba.
Haka ya yi ta yawo a titunan Abuja ko zai hadu da ita.
Da hakarsa ta kasa cimma ruwa, sai ya bullo da sabuwar hanya ta amfani da intanet.
Bai yi wata-wata ba ya yi bidiyo wanda a ciki yake bayyana kaunarsa ga Hanan tare da sanar da cewa zai bayar da sadakin shanu 150 idan ta yarda ta aure shi.
Ya kuma wallafa bidiyon a intanet.
“Ina kan amfani da kafafen zumunta ne na samu labarin cewa an yi mata baiko, sai na hakura.
“Da na yi tunanin na je gidan kakanninta a Yola na kulla dangataka da ita ya hanyar danginta.
“Yanzu da za ta yi aure, ina mata addu’ar zaman lafiya kuma ina farin cikin bayar da gudunmuwar shanu 50 domin bikin daurin auren”, inji shi.
Abdullahi ya shafe tsawon lokaci a Abuja yana bin wuraren bukukuwa ta taruka har zuwa lokacin bullar cutar coronavirus ta tilasta masa komawa Yola.
Kwarin gwiwa
Abdullahi na jin kwarin gwiwa, don haka bai damu da sanya sabbin kaya da yin shiga ta kasaita ba.
Damuwarsa kawai ita ce ya hadu da Hanan gaba da gaba, ya bayyana mata abin da ke zuciyarsa.
Idan ma ta ki amincewa, kalamansa na iya yin tasiri a kanta har watakila ya samu shiga a zuciyarta.
“Da zan bayyana mata sona in kuma jira ta ba ni amsa. Ko da za ta ki yarda ban damu ba saboda wani lokaci a hankali so ke shiga zuciya.
“Haduwa da ita na da muhimmanci domin in samu bayyana mata abin da ke raina, ko da sawa za ta yi a ba ni kashi.
“Da zan gamsar da ita ta amsa bukatata. Idan kana son mace, ba lallai ne ta yarda nan take ba, amma a hankali daga baya za ta iya fara son ka.
“Buharin da na sani ba zai damu don ya ba ni diyarsa ba, matukar tana so na, saboda shi na al’umma ne”, inji shi.