✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan neman aikin dan sanda a Najeriya

Hukumar ‘yan sanda ta Najeriya (NPF) ta sanar da fara daukar ma’aikata na shekara ta 2020, rukunin kurata ga masu bukata. An bude daukar aikin…

Hukumar ‘yan sanda ta Najeriya (NPF) ta sanar da fara daukar ma’aikata na shekara ta 2020, rukunin kurata ga masu bukata.

An bude daukar aikin ne daga ranar 14 ga watan Yuli zuwa 23 ga watan Agusta, 2020, kuma kyauta ne cike takardar neman aikin.

Yadda za a cike aikin dan sanda na shekarar 2020

  • Dole ne sai kana da adireshin email da lambar shaidar dan kasa (NIN) kafin ka soma cike aikin.
  • Wajibi ne a cike gurbin neman aikin a shafin intanet.
  • A shiga wannan adireshin www.policerecruitment.gov.ng domin cike gurbin aikin.
  • Idan aka shiga adireshin sai a cike takardar neman aikin da ke intanet (ka tabbatar ka karanta abin da ka cike sosai kafin ka aika da takardar).
  • Ka tabbatar ka sanya bayananka kamar yadda suka fito a kwamfuta sannan ka aika ta email dinka (kar a manta a kwafa a kuma adana lambar da rajistar ta nuna saboda amfanin gaba)
  • Ba za ka iya amfani da email daya ko lambar NIN daya ba ka nemi gurbin aiki fiye da daya.
  • Sannan ba za a iya amfani da sauran bayananka ka nemi gurbin aiki fiye da daya ba.
  • Don neman bayani ko wani taimako sai a tuntubi lambar 08100004507 ko kuma a tura sakon email zuwa ga:
    [email protected] ko kuma [email protected]