✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantun ’ya’yan makiyaya a Jigawa na fama da karancin malamai

Karancin malaman Ingilishi da Lissafi ya addabi makarantun ’ya’yan makiyaya a Jihar Jigawa duk da makudan kudadEn da hukuma take kashewa wajen sayen kayan koyarwa…

Karancin malaman Ingilishi da Lissafi ya addabi makarantun ’ya’yan makiyaya a Jihar Jigawa duk da makudan kudadEn da hukuma take kashewa wajen sayen kayan koyarwa a makarantun. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Ilimin ’Ya’yan Makiyayan ta Jihar Jigawa Malam Shehu Garba Sakwaya a wata hira da ya yi da wakilin Aminiya, inda ya ce suna da makarantu 323 ginannu, kuma daga cikinsu 80 suke da kyau yanzu haka wadanda ake iya yin karatu a cikinsu, amma dukkan sauran sun koma yin karatu a gindin bishiya saboda makarantun sun lalace ba sa samun kulawar da ake bukata.

Shugaban hukumar ya ci gaba da cewa a gaba daya makarantun, suna da malamai 621, inda saboda karancin malaman ya sa a wasu makarantun ma babu malaman Ingilishi da Lissafi wadansu suke kula da makarantun a matsayin jagororin makarantun.

Ya ce a bara sun sayi kayan aiki na Naira miliyan 78 kuma a bana za su kashe Naira miliyan 98 yayin da suka kashe Naira miliyan 4.3 wajen gyaran makarantun ’ya’yan makiyaya da ke jihar.

Shehu Garba ya kara da cewa sun ware Naira miliyan 13.6 domin gyaran makarantun ’ya’yan makiyaya 8 da ke kananan hukumomin Birnin Kudu da Gagarawa da Roni da Gumel, da Kirikasamma da Kazaure da Birniwa.

Ya nuna damuwarsa game da lalacewar makarantun musamman a lokacin damina, inda idan ana yin ruwa ba sa samun natsuwa.

Da ya juya kan batun tallafin da Gwamnatin Tarayya take bai wa ’ya’yan makiyayan ta bangaren ilimi kuwa cewa ya yi ta tallafa wa dalibai 44,250 inda suka amfana da kayan makaranta da jakunkuna da takalma guda 29880,000 a fadin jihar.