Makarantu masu zaman kansu a Jihar Kano sun nemi jihar ta yafe musu biyan harajin zangon karatu na biyu saboda kullen COVID-19 da aka yi.
Shugabar kungiyar masu makarantu a jihar, Hajiya Maryam ta yi rokon ne saboda rashin biyan kudin makaranta da bullar annobar ta haifar.
Ta yi kiran ne bayan Gwamnatin Jihar ta yi alkawarin tallafa wa malamai da sauran ma’aikatan makarantun kudi domin rage musu tasirin kullen.
Jihar ta bayyana haka ne yayin rabon kayan kariyar lafiya (PPEs) ga makarantun gwamnati da masu zaman kansu 538 a fadin jihar.
Tuni dai jihar ta fara feshin magani a makarantun da ke jihar a shirinta na bude su ga daliban ajin karshe na sakandare a ranar 10 ga Agusta.
Gwamna Abdullahi Ganduje ta bakin mataimakinsa Nasir Yusuf Gawuna yayin raba kayan ya ce masu makarantun kudi sun koka kan kalubalen da annobar COVID-19 ta kawo musu.
Ya ce rabon kayan kariyar na daga cikin shirye-shiryen jihar na komawar daliban ‘ya ajin karshe makarantun don fara jarabawa.
Ya bukaci wadanda suka samu tallafin su yi amfani da su yadda ya jace, su kuma bi ka’idojin da masana harkar lafiya suka bayar domin jihar na dab da ganin bayan cutar.
Kayan da aka rarraba sun hada da takunkumai, sinadarin tsaftace hannu, kayan wanke hannu da kuma na’urar gwajin zafin jiki.
Kwamishinan Ilimi Sunusu Sa’id Kiru, ya ce daga cikin dalibai 27,454 da za su rubuta jarrabawar WAEC a jihar, kimanin 11,400 daga makarantun gwamnati suke yayin da 16,460 suke makarantu masu zaman kansu.
Shi kuwa Kwamishinan Lafiya na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa tabbaci ya bayar cewa za su tabbatar an tantance daliban yadda ya kamata tare kuma da tabbatar da cewa suna wanke hannu akai-akai.