✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantun allo da rayuwar almajirai a Jihar Sakkwato

Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da ake samun tururuwar kananan yara da ake turawa daga wasu garuruwa da kauyuka da sunan karatun allo,…

Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da ake samun tururuwar kananan yara da ake turawa daga wasu garuruwa da kauyuka da sunan karatun allo, inda kuma suke fama gararamba a kan tituna da gidajen jama’a don barar abinci.

Umar yaro ne dan shekara 7 da aka kai shi Sakkwato daga Karamar Hukumar Isa. Ya ce yana almajirci ne a birnin Sakkwato kullum daga karfe 9 na safe har 2:30 na rana yana bara kan titi don nema wa kansa abincin da zai ci.

Aminiya ta same shi abin tausayi yana sanye da tufafin da ba za su kare shi daga jin sanyi ba, a yanzu da ake fama da hunturu, yana cikin daruruwan yaran da ake turowa da sunan yin karatun Alkur’ani.

“Nakan tafi nan da can ina yawon barar  abincin da zan ci. Mafi yawan abincin da nake samu ragowa ne na wadansu,” inji shi.

Umar ya ce an kawo shi birnin Sakkwato ne daga Karamar Hukumar Isa shekara biyu da rabi da suka wuce. Bayan ya gama yawon bararsa da rana yakan tafi wurin malaminsu ya biya masa karatu. Ya ce kuma yakan bai wa malamin nasu Naira 50 a wani lokaci ba kullum ba. Da maraice Umar yakan koma gida da karfe biyar ya yi karatu har zuwa karfe takwas ya kuma tusa wani.

Wani almajirin mai suna Bashiru dan shekara bakwai, an dauko ne shi daga kauyen Unwala a Karamar Hukumar Illela, aka kawo shi wajen wani malami a Sakkwato. Ya ce ya kwashe shekara uku yana yawon bara a titi.

Ya bayyana yadda yake zagayensa da cewa: “Mukan yi karatu da safe da rana da dare sannan muna samu lokacin yin barar abinci. Ina zuwa tashar mota da wuraren sayar da abinci don in samu wanda zan ci, ina iya kwashe dukan yini kafin in koma makaranta.”

Kabiru Shehu almajiri ne dan shekara 14 da ya zo daga Kebbi, inda ya ce yana tallar masar Malam. Ya ce “Na kwashe fiye da shekara biyar a garin nan, kuma bayan mun kare karatun safe nakan dauko masar Malam in zagaya cikin mutane tare da almajirai muna talla, idan an saya in ba su sadaka, in ta kare mu koma gida.”

Aminiya ta gana da Malam Aliyu Sheikh Ibrahim Tunau Goronyo, shugaban makarantar allo ta Zawiyya a Karamar Hukumar Goronyo, kuma shi ne jagoran Darikar Tijjaniya a karamar hukumar a  ranarLitinin da ta gabata, inda ya ce ya gaji mahaifinsa ne da ya shekara kusan 30 da rasuwa. Ya ce yau shekara 10 ke nan da suka fara karantar da almajirai a makarantarsu.

Ya ce “Na yi kokari a makarantata in hana almajiraina yawon bara, amma iyayen yaran sun ki bayar da goyon baya, duk da a cikinsu akwai masu iya daukar nauyin karatun ’ya’yan nasu.”

Ya ce “Almajirai na shigowa daga garuruwa domin neman ilmin addini. Muna da yaran da suka zo a kauyukan Dimbiso da Duhuwar Gumsa da Duhuwar Marnawa da Nasarawa a Karamar Hukumar Wurno, akwai wadansu daga Giyawa da Takakume  da Falaliyawa da Waran Kai da Gidan Hashimu da Uda a nan cikin Goronyo har a Marnona da sauransu. Kowane gari za ka samu sun kawo mana yaro daya ko biyu ko 10 ko 20, akwai garin da ke da kusan mutum 70. A yanzu muna da almajirai sun kai 200, duk mako ana kawo mana yara daga daya zuwa goma. Wadansu daga cikin yaranmu tunda suka tafi hutun Sallah Babba ba su dawo ba, domin suna aikin fadama.”

Da ya juya kan tsarinsu na karbar almajirai, ya ce “Akwai fom da muke cikawa na ka’idojinmu kafin yaro ya shiga makaranta. Fom din yana dauke da sunan yaro da mahaifi da adireshi  da bayanin ko yaro na da ciwo ko babu, da sanin ko akwai bukatar karatun boko da kudin rajista Naira dubu daya da kudin fom Naira 200, sannan kuma muna karbar Naira 200 duk wata daga hannun uban yaro domin ajiyewa a saya wa yaro magani. Mun gindaya sharadin almajirinmu ba ya zuwa kasuwa, wadansu almajiranmu suna zuwa bara amma ita kasuwa da yara ke zuwa yin sata ko talla, ba mu amince ba. Duk yaron da ka gani a kasuwa ba namu ba ne, wadanda ba a daukar nauyinsu suna tafiya neman abinci, wadansu iyaye ba su son ’ya’yansu su tafi bara, wadansu kuwa sun ce ba su da hali. Wadansu na ganin tauye yaro ne don wanda ke yawo ya fi samun abinci.”

“Iyaye masu daukar nauyin ’ya’yansu za su kawo kanzo da shinkafa da gari da kudi su bai wa yaro ya rika ci safe da rana da dare,” inji Malam Aliyu.

Kan kudin mako da aka ce suna karba, da ake aza wa yara su biya, sai ya ce “Ga hannun iyayen yara muke karbar kudin fom, mun fada musu abin da muke yi da kudin. Idan yaronsu ba ya da lafiya za mu saya masa magani da kudin matukar maganin bai kai Naira dubu daya ba. Idan ya kai haka kuwa, to uban yaro zai saya.”

“Akwai malamai masu sanya yaro ya rika ba su Naira 50 ko 30 duk rana. Mu ba haka muke yi ba, muna da wakilai a garuruwa da sunayen yara, duk wata suna tafiya inda uban yaro suke su karbo mana kudin. Ba mu aza wa yaro komai, ina fada wa iyayen yara haka. Akwai wani malami ya tambaye ni, da bakinsa ya ce ya san ina da yara da yawa nawa suke kawo mini duk mako? Na ce ba na aza komai, ya ce shi duk mako (Lahadi) yaran suna kawo masa Naira 50, ya samu abin rage lalura. Ya ce in rika yin haka, na fada masa in na buda wannan babi komai ya lalace, don ko sata ko sadaka sai sun kawo. Na ce ba ruwana da yi musu azaba ba bisa hakki ba. Ina karbar goron sauka dai in yaro ya sauke. Mukan je mu yi masa walima ni da abokan karantarwata,” inji shi.

Da ya koma kan matsalar da almajirai ke fuskanta, ya ce ba za ta wuce ciyarwa ba. Ya ce duk yaron da ka sake shi ya je ya yi bara, ba a san halin da zai shiga ba. “Ko halal ko mene ne in ya ga wurin sata ya yi, sai ka ga ana kawo karar yara sun saci tuwo da kudi. Yaro ya fita bai samu abinci ba, in ya ga na wani sai ya dauke. Ga rashin lafiya, sai ka samu yaro 10 ko 20 duk ba lafiya lokaci guda. Muna da likita mai taimaka mana. Iyayen yara na da matsala, ba su bari a yi tsari mai inganci, jahilci ya ki bari su fahimci abin da muke son a yi da zai taimaka wa karatun. Sai su dauka abu ne za a kawo masu sabo, wasunsu na cewa ba su taba ganin makarantar allo da karbar kudi ba,” inji shi.

Dangane da hadin kan malamai don a yi gyara kuwa, sai ya ce “Ba za mu yi daidai da sauran mutane ba, domin wadansu ba karatun almajirai ya dame su ba; suna da manufofi da buri don haka suke sakinsu su je talla. Mu ko aiki muka sanya yaro za mu ciyar da shi. Tunda safe za ka ga yaro yana bara a wajen mai abinci, kasan ba karatu ne manufa ba.”

“Ko da aka fara tsarin karatun boko da allo, UNICEF ta zo mana da tsarin tana tallafa mana, wakilansu na zuwa amma a gwamnatance jiha da tarayya ba wanda ya kawo mini tallafin hada karatun boko da allo, duk mai son tallafa wa jinsin dan Adam abu ne mai kyau. Rashin tallafin da muke samu ya kasance malamanmu 10 yanzu sun koma 6. Wannan abun ya kawo mana rauni a karatun,” inji Malam Aliyu Ibrahim.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Bishop din Katolika na Sakkwato Fada Matthew Hassan Kuka kan zargin ya ce zai dauki nauyin koya wa almajirai sana’a, ya musanta wannan zance.

Ya ce “Ka ji wannan maganar daga bakina? Ka je ka tambayi wadanda suka yi maganar, inda na yi wannan maganar ka nemi karin bayani. Ba su ce ga inda na yi bayanin ba ko ga inda na samo kudi. Kai ko san yawan mutum miliyan 10, da har wani ya ce na ce zan koya masu sana’a? Kai ka bar wannan maganar.”