Hukumar tsaro ta ‘Civil Defence’ (NSCDC), ta ce makarantu 62,000 a fadin Najeriya na fuskatar barazanar tsaro.
Kwamanda-Janar na NSCDC, Ahmed Audi ya ce an gano hakan ne bayan wani bincike da hukumar ta gudanar kan yanayin tsao a makarantun kasar.
“Mun yi bincike kan hadarin da makarantu a fadin kasar nan ka iya fadawa sakamakon matsalar tsaro, shi ya sa muka bullo da sabbin matakan tsaron su.
“Binciken ya gano akwai makarantu sama da 81,000 a Najeriya amma abun mamaki shi ne 62,000 ba su da kariya ko tsaro na zahiri kamar katanga da sauransu.
“Hakan na nufin yara suna cikin hadarin hari a kodayaushe kuma yawancin makarantun na gwamnati ne,” a cewarsa.
Da yake jawabi yayin kaddamar da sabbin motoci 200 ga kananan jami’an hukumar a Abuja ranar Talata, Kwamanda-Janar din ya ce ya zama dole a kara himma wajen kawo sabbin matakan kare makarantu a Najeriya.
Audi ya bayyana cewar hukumar ta fara shirye-shiryen gabatar da kayan aikin tsaro na sanya ido a kan kayan gwamnati a fadin kasar.
“Najeriya na fama da rikice-rikice; Mun gano cewar dole ne sai an koma tushe don yin aiki cikin fikira da bullo da sabbin hanyoyin dakile matsalolin tsaro”.
Ya yi kira da a bullo da sabbin hanyoyin yaki da ta’addanci ciki har da karfafa wa jami’an tsaro gwiwa duba da yadda matsalar ke kara ta’azzara.