✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Sojin Sama ta yi bikin saukar karatun Alqur’ani ga dalibanta

  Makarantar Sojin Sama da ake kira  Air Force  Comprehensibe School da ke Kano, ta yi bikin saukar karatun Alkur’ani Mai girma na dalibai 74…

 

Makarantar Sojin Sama da ake kira  Air Force  Comprehensibe School da ke Kano, ta yi bikin saukar karatun Alkur’ani Mai girma na dalibai 74 tare da walimar kammala karatunsu a ranar Asabar da ta gabata.

Bikin saukar karatun wanda ya samu halartar Kwamandan Sojin Sama da ke Kano da wadansu manyan baki daga sassan kasar nan, shi ne  na farko da makarantar ta gudanar  tunda aka fara karatun Alkur’ani  da fannin Islamiyya a cikinta.

Dalibai maza da mata sun gabatar da karatun Alkur’ani da Hadisi da Sira, sannan an yi jawaban zaburar da daliban game da muhimmancin neman ilimin addini da na zamani ta yadda rayuwa za ta zamo mai albarka.

Tun farko a jawabin maraba, Kwamandan makarantar, Adamu Abdul ya ce  saukar karatu ita ce ta farko kuma za a ci gaba ya gudanar da ita duk shekara ta yadda za a bunkasa ilimin addinin Musulunci da inganta tarbiyyar yara domin su zamo jakadu nagari a kasa baki daya.

Sai ya yaba wa wadanda suka tsaya wajen tabbatar da ganin an gudanar da biki cikin nasara kuma ya gode wa daukacin bakin da suka halarci saukar karatun musamman Kwamandan Sojin Sama da ke Kano da wadanda suka halarci bikin daga sassan kasar nan. A karshe ya hori daliban da suka yi saukar kan su yi aiki da ilimin da suka koya a makarantar.

Sauran wadanda suka gabatar a jawabi a wurin sun hada da Malam Muhammad Zangina Usman, Shugaban Makarantar Islamiyya ta Ubayyu bin Ka’ab wanda ya yi jawabi kan muhimmancin karatun Alkur’ani da Dokta Ibrahim Ilyas Adam na Jami’ar Maitama Sule wanda ya yi jawabi kan amfanin ilimi ga rayuwar dan Adam.

Daga bisani an rarraba kyaututtukan yabo ga hazikan dalibai da malaman makarantar.

Wakilinmu ya zanta da Kwamandan Makarantar Adamu Abdul da Limamin Makarantar Malam Habib Haruna Ibrahim inda suka nuna farin ciki kan yadda bikin ya yi nasara, tare da nanata cewa da yardar  Allah makarantar za ta ci gaba da gudanar da  bikin saukar karatun.