✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Kuratan Soji ta gina burtsatse da ba da tallafin magunguna ga jama’ar Zariya

 Aranar Alhamis din makon jiya ne Makarantar Horar da Kuratan Soji da ke Zariya, ta tallafa wa al’ummar Unguwar Gyallesu da Tudun Wada da kyautar…

 Aranar Alhamis din makon jiya ne Makarantar Horar da Kuratan Soji da ke Zariya, ta tallafa wa al’ummar Unguwar Gyallesu da Tudun Wada da kyautar magunguna, tare da kaddamar da rijiyar burtsatse a Jushin Waje da ke Sabon Gari, Zariya, kuma ta gudanar da aikin tsabtace gari inda ta kwashe juji.

Da yake jawabi wajen kaddamar da shirin Birgediya Janar Hassan Mamman Lai Muhammad (mai ritaya), wanda ya wakilci Kwamandan Makarantar Kuratan ya ce makasudin bikin shi ne domin tunawa da Ranar Sojoji da ake gudanarwa ranar 6 ga Yulin kowace shekara.

Birgediya Janar Hassan Mamman Lai Muhammad (mai ritaya), ya ce Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf Burutai ya ce za a rika gudanar da wannan shiri duk shekara domin karfafa dangantaka a tsakanin sojoji da fararen hula. Janar Mamman Lai ya ce aikin kwashe sharar zai samar da tsabtataccen muhalli kuma zai kara wa jama’a kwarin gwiwa domin su ma su rika yi.

Ya ce an gina wa mutanen Jushi rijiyar burtsatse ce domin samar musu da ruwan mai kyau, don haka ya yi kira ga mazauna yankin su yi amfani da ita yadda ya dace.

A jawabin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris wanda Fagacin Zazzau Alhaji Abdullahi Muhammad ya wakita ya yaba wa Kwamadan inda ya ce an gudanar da bikin a lokacin da ya dace saboda mutane da dama ba su samun zuwa asibiti sakamakon matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan.

Rundunar Sojin ta gudanar da aikin duba marasa lafiya tare da ba su magunguna kyauta a makarantar firamare ta tunawa da marigayi Ahmadu Gyallesu tare da sharar gari daga Shataletalen PZ zuwa Shataletale Agoro da ke Tudun Wada, Zariya.