Makarantar Nazarin Addinin Musulunci ta Jama’atu College da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta yaye dalibai 692 a karshen makon jiya.
Da yake jawabi a wajen taron yaye daliban Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna na kan Harkokin Makarantun Islamiyya Malam Isma’ila Mainasara Muhammad ya ce babban kudirin gwamnatin Jihar Kaduna, kan makarantun Islamiyya shi ne su samu ci gaba irin na zamani.
Ya ce gwamnatin tana tsare- tsare don ganin makarantun Islamiyya da makarantun Allo sun shiga tsarin gwamnati a jihar, don ganin daliban makarantun sun zama kamar daliban makarantun zamani, ta yadda su ma za su rika samun aikin gwamnati.
Ya yi kira ga makarantun Islamiyya da malaman makarantun su ci gaba da koya wa yara tarbiyya da zaman lafiya, domin a ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.
A jawabin daya daga cikin shugabanin makarantar Malam Nuhu Liman Saminaka ya ce suna kokarin kammala ginin mazaunin wannan makaranta na dindindin.
Ya ce manyan ’yan siyasa da masu hali na yankin sun taimaka wajen sayen filin gina makarantar kan Naira miliyan 2. Kuma makarantar ta yi kokari wajen kara sayen wasu filaye da ke kusa da filin da ake ginin makarantar tare da kokarin gina ajujuwa 3 da ofishin malamai.
Ya ce nan ba da dadewa ba makarantar za ta koma mazauninta na dindindin.
Ya yi kira ga iyayen yara su kokarta su sanya ’ya’yansu a makarantar domin su karanci addini da tarbiyya da za su taimaka wa rayuwarsu a nan duniya da Lahira.
Tun farko a jawabin Mataimakin Shugaban Makarantar Malam Abdullahi Shu’aibu Liman Saminaka ya ce a bana a bangaren babbar sakandare sun yaye dalibai 45, a karamar sakandare sun yaye dalibai 250, sai bangare firamare sun yaye dalibai 397.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da kasa baki daya su kula da addinin Musulunci sosai, domin shi ne zaman lafiyar al’umma a duniya da Lahira.