✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar firamare ta yi bikin cika shekara 100 a Kaduna

An fara karatu a makarantar ce a shekarar 1922 da dalibai 14.

Daruruwar al’ummar garin Makarfi ne suka halarci bikin cika shekara 100 da kafa makarantar firamare midil ta Makarfi a Jihar Kaduna.

A cewar wadanda suka shirya taron an fara karatu a makarantar ce a shekarar 1922 da dalibai 14.

Da yake jawabin bude taron, shugaban shirya taron, Garkuwan Zazzau Alhaji Suleiman Abdulkadir ya ce makarantar ta yaye dalibai masu yawa da suka zama manyan mutane a jihar dama kasa baki daya.

Ya kara da cewa tsofaffin daliban sun shirye bikin ne domin hadin kai tare da taimakawa tsohuwar makarantarsu.

A cewarsa, tuni an fara gyarar makarantar bayan samun tallafi daga wasu daliban, inda ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka ba da taimakonsu domin gyarar makarantar.

A jawabin Mai martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli kira ya yi ga iyaye su tabbatar sun ilimantar da ’ya’yansu a ilimin boko da na addini.

A cewar Sarkin, babban abin da iyaye za su ba ’ya’yansu a rayuwa shi ne ilimi domin su zama mutanen kirki.

Ya bayyana cewa baya ga Zariya babu wani gari a yankin da ke da fitattun mutane irin garin Makarfi.

Sarkin ya yaba wa Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi bisa ayyukan alheri da ya zartar a lokacin da yake gwamna.

A jawabin tsohon Gwamnan Jihar Ahmed Mohammed Makarfi wanda tsohon dalibi ne a makarantar ya ce akwai bukatar a yi rajistar kungiyar tsofaffin daliban makarantar domin su ci gaba da taimaka wa makarantar.

Sai shugaban kwamitin kudi na taron Lawal Umaru Meyere ya tabbatar da cewa za su yi duk mai yiwuwa waje ganin an yi rajistar kungiyar.

Wasu daga cikin tsofaffin daliban makarantar baya ga Sanata Ahmed Makarfi su hada da Sanata Yusuf Makarfi a Jamhuriyya ta Biyu da Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa Farfesa Abubakar Rasheed da Alhaji Garba Bala Makarfi da sauransu.