A wannan mako, ina so ne mu ci gaba da koyarwar da muka soma watanni kadan da suka gabata. Muna cikin mayuwacin hali a wannan lokaci, abu daya da zai ba mu nasara cikin rayuwa a wannan zamani kuwa shi ne sanin makaman yakinmu da kuma yadda za mu yi amfani da su. Mun riga mun gabatar da wannan bincike da muka soma, har ma mun dauki kaddn daga cikin wadannan makamai. A yau, bisa ga yardar Allah, za mu ci gaba da bincike a kan wannan kan magana: wato Makaman yaki na Kirista, wadannan makaman yaki, asiri ne da Allah da kanSa Ya shirya ga dukkan masu binSa. A yau za mu yi kokari mu duba makami na biyu daga cikin wadannan makamai.
Sulke na Adalci: Sulke dai; ga wanda ya san makaman yaki, makami ne da kan kare kirjin mutum daga kowace kibiya, mashi ko adda, wadanda magabci yakan iya harbowa, ko ya jefo, yawancin lokaci dai, Shaidan yakan kawo harinsa ta wurin harbin kibiyoyi ne bi-da-bi, kuma a-kai-a-kai domin ya iya rikitar da wadanda yake fuskantarsu a bakin daga. Wadannan makamai da Iblis yake amfani da su domin yakar masu bin Yesu Kiristi, sun kunshi kalubalen da muke fuskanta a yau da kullum, cikin zama ko a wurin aiki, ko a kasuwa ko a cikin siyasa, ko wajen neman aiki da sauransu. Wani lokaci su zo ta fannin cin mutuncin da za a yi mana, wani lokaci danniya da za a yi, abin da ya dace ka samu, kana gani sai a bai wa wani, a wani jikon kuwa jarrabawa ce iri-iri da za ta zo ga mutum, wani lokaci sukan iya zuwa ta fuskar rashin abinci, ko rashin kudi, a cikin irin wannan bukatun ne sai ka iske kanka cikin wani ofis inda akwai kudi ko kayan abinci, idan har ba ka lura ba za ka iya jarabtuwa har ya kai ka ga sata; ainihin abin da Shaidan yake so ka yi ke nan. Duk abin da ba zai gamshi Ubangiji Allah ba, shi ne Shaidan ke so ka yi. Sai mu lura da irin wadannan hanyoyi na Iblis mai rudin mutane. Ina so mu lura da abu guda, wannan kuwa shi ne, Sulke ga wanda ya san yaki, makami ne wanda ya zama kamar dole kowane mayaki ya dauka ya rataya domin wurin da yake karewa. Sulke dai ana sa shi ne domin ya rufe kirjin mutum, musamman a filin daga koyaushe, da yake ba ka san ko ta ina ne kibiyar da Shaidan zai harbo za ta fito ba, sai mu tuna cewa abin da Shaidan yake da niyar yi koyaushe, shi ne ya bata tsakanin mutum da Allah. Idan har ka bar shi, to babu shakka zai rinjaye ka. Tambayar da ya kamata mu amsa domin mu fahimta sosai, ita ce, yaya wannan Sulke yake aiki? Idan mun tuna, maganar Allah tana cewa, wannan Sulke din shi ne adalci. Mene ne adalci? A cikin Littafin Kubawar-Shari’a 6 : 25, maganar Allah tana cewa, “Zai zama adalci gare mu kuma, idan mun kiyaye dukkan wannan umarni garin mu aikata a gaban Ubangiji Allahnmu, kamar yadda Ya umarce mu.” Adalci shi ne aikata abin da Allah Ya umurci mu yi, kowane mutum da ya kiyaye maganar Allah da umarninsa kamar yadda yake cikin Littafi Mai tsarki, wannan mutum mai adalci ne a gaban Allah, haka idan har mun sa nufin Ubangiji Allah a gaba, gaskiya babu shakka shi Yesu Kiristi ubangijinmu zai zama mana kariya daga dukkan hari da Iblis zai kawo mana. Yin biyayya ga umarnin Allah abu ne mai muhimmanci sosai a wurin Allah. Yana gamsar da Ubangiji Allah sosai a koyaushe. A cikin Littafin Zabura 11 : 7 haka nan maganar Allah ta koya mana cewa: “Gama Ubangiji Mai adalci ne; Yana kaunar adalci, Mai zuciya sosai za shi ga fuskarsa.” Ashe duk mai adalci, yana da wannan tagomashin, na sanin cewa zai ga fuskar Allah, sanin cewa Allah Yana kaunar mai adalci abu wanda ya kamata ya sa mu ci gaba da tafiya ciki. Mu tuna cewa ba wai akwai sauki ba ne, muna cikin mawuyacin lokaci, Shaidan yana gaba da masu bin Yesu Kiristi, yakan yi aiki da wadansu domin ya gurguntar da tsayuwarmu a gaban Ubangiji Allah, kada mu ba shi dama ko kadan. Idan har za mu iya jure wahalar nan ta dan lokaci, Ubangiji Allah zai tashi a madadinmu, a lokacin ne sauran jama’a za su san cewa muna bauta wa Allah Mai rai, Mai iko duka, kada mu karaya, Ubangijinmu da Allahnmu bai bar mu ba. kaunar yin adalci tana da amfani sosai ga kowane mai bin Yesu Kiristi, kada mu yarda Shaidan ya kazantar da mu da kwadayin kayan duniya wadanda ba za su dauwama ba ko kadan. Ubangiji Allah Ya san muna da bukatar wadannan abubuwa da za su taimake mu rayuwa cikin wannan duniya, amma Ya ce mana a cikin Littafin Matta 6 : 25 – 33: “Domin wannan fa ina ce muku, kada ku yi alhini saboda da ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha, ko saboda da jikinku abin da za ku yafa, Rai ba ya fi girman abinci ba? Jiki kuma ba ya fi tufafi ba? Ku duba tsuntsaye na sama, ba sukan yi shuka ba, ba sukan yi girbi ba, ba sukan tattara cikin rumbuna ba, amma Ubangiji na sama Yana ciyar da su, ku ba ku fi su daraja da yawa ba? Wane ne fa daga cikinku, bisa ga alhininsa, yana da iko ya kara ko kamu daya ga tsawonsa? Don mene ne kuma kuke alhini da zance tufa, ku lura da furanni na daji, girman da suke yi; ba su yi wahala ba, ba su yi kadi ba, duk da haka ina ce muku, ko Sulaimanu da darajarsa duka, ba ya yafa kawa kamar guda dayansu ba. Idan fa Allah Yakan yi wa ganyayyakin saura sutura haka, abin da ke rayuwa yau, gobe ana jefawa cikin tanderu, balle ku, ku masu kankantar ban-gaskiya? Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, me za mu ci? Ko kuwa, Me za mu sha? Ko kuwa da mene ne za mu yi sutura? Gama wadannan abubuwa duka al’ummai suna ta bida; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar wadannan abubuwa duka. Amma ku fara bidar mulkinSa da adalcinSa; wadannan abubuwa duka fa za a kara maku su.” Mu lura sosai, akwai abubuwan da a gaskiya mutum zai iya jarabtuwa da su, amma idan madogararmu Allah ne, za mu zama masu nasara. Idan Allah Ya bar mu cikin masu rai za mu ci gaba mako mai zuwa daga inda muka tsaya.
Mu ci gaba da yin addu’a domin kasarmu, musamman Shugaban da Allah Ya ba mu wato Shugaba MuhammaduBuhari da dukan wadanda suke aiki tare da shi, bari Allah Ya kara musu hikima har su iya kawo ci gaba a wannan kasa, mu yi addu’a kuma domin mu talakawan wannan kasa musamman wadanda suke fama da rashin abinci a gidajensu. Gaskiyar ita ce akwai yunwa a kasar nan yanzu, dole ne mu tallafa wa juna, muna kuma rokon Allah Ya kawo mana sauki. Ubangiji Allah Ya taimake mu duka, amin.
Makaman yaki na Kirista (8)
A wannan mako, ina so ne mu ci gaba da koyarwar da muka soma watanni kadan da suka gabata. Muna cikin mayuwacin hali a wannan…