Kamar yadda muka soma koyarwa a kan Makaman Yaki na Kirista, ina so mu ci gaba da gane wadansu abubuwa:
Dole ne kowane mai bin Yesu Kiristi ya san cewa a kullum; yana fuskantar yaki ne cikin duk rayuwarsa a wannan duniya.
Wannan yaki kuwa ba zai kare ba har sai ranar da ubangijinmu da mai cetonmu ya dawo domin ya dauke mu zuwa wurinsa, ya kai mu inda ya riga ya shirya wa duk masu bin sa.Yakin nan ba na nama da jini ba ne, a’a, amma yaki ne na ruhaniyya: a cikin Littafin Galatiyawa 10: 3, maganar Allah tana cewa – “Gama ko da muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaki bisa ga jiki ba” haka nan kuma cikin Littafin Afisawa 6: 12; maganar Allah na cewa “Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniyya na mugunta cikin sammai.”
Mai yiwuwa ne wani zai yi tambaya kamar haka: yaushe ne masu bin Yesu Kiristi suka shiga cikin wannan yaki? To bari mu sani da kyau cewa daga ran da mutum ya yi imani da shirin Allah domin ceton duk duniya; kowane mutum da ya rigaya ya ba da gaskiya cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, kuma wannan Yesu Kiristi ya mutu domin zunubansa, shi ne kuma ya zama dalilin cetonmu daga mutuwa ta biyu wato rabuwa da Allah ke nan; tun daga wancan lokacin ne masu bin Yesu Kiristi suka shiga dagar yaki. Wannan yaki ba kamar yadda duniya take tsammani ba ne, wannan ba na daukar bindiga da harsashi ba ne, ko kuwa daukar takobi ko adda ba ne, ban a duk irin wadannan makamai masu linzami da mutum ya kera ba ne, wadannan irin makamai ba su da amfani ko kadan a cikin irin wannan yaki kuma ba za su taba yin amfani a wannan yaki ba. Abin da ya sa wadannan irin makamai ba za su taba amfani ba, ko kadan kuwa shi ne, wannan yaki na ruhu ne ba na nama da jini ba ne. Magabcin da muke fuskanta ba nama da jini ba ne kawai a’a, Shaidan ne da kansa da kuma sauran wadanda suka yarda da shi, shi ya sa makamai kirar dan Adam ba za su yi amfani ba ko kadan.
Mutum ba ya yaki da kansa; sai dai ko idan shi mahaukaci ne: to da wane ne m ke yaki? Wane ne wannan magabcin? Yaya mutum zai gane wannan magabcin idan har ya bayyana? Wane irin makami ne za mu dauko wanda za mu iya yin amfani da shi domin mu iya cin nasara? Wadannan tambayoyin ne za mu yi kokari ua ga ko za mu iya amsa su.
Da wane ne muke yaki:
Da Iblis -Shaidan: tun daga farko a cikin Littafin Farawa sura uku aya kuma ta goma sha hudu zuwa aya ta sha biyar (3: 14 – 15) maganar Allah tana cewa “Ubangiji Allah kuma Ya ce wa macijin, tunda ka yi wannan, la’ananne ne kai cikin dukan bisashe da kowane dabba; rub-da-ciki za ka yi tafiya, za ka ci turbaya kuma dukan muddar ranka: tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka da tsakanin zuriyakka da zuriyarta kuma, shi za ya kuje kanka, kai kuma za ka kuje duddugensa.” Mu sani fa cewa wannan magabtakan ta soma ne tun daga farkon farawa; a lokacin da Shaidan ya shigo cikin tunanin mutum, ya ba shi shawara ya ki bin umarnin da Allah Ya ba shi. Idan mun tuna lokacin da Allah Ya halicci mutum Ya sa shi a cikin gonar Adnin; sai Ya ba shi umarni cewa an yarda masa ya ci daga cikin itatuwa na cikin ganar Adnin, amma daga cikin ’ya’yan itacen da ke tsakiyar gona, ba a yarda masa ya ci ba; shi Iblis abin da yake so ke nan – yin gaba da dokokin Allah, haka ya rudi mutum ya karya dokar da Allah Ya ba shi. Tun daga lokacin ne magabtaka ta soma tsakanin Allah da Shaidan da duk wanda ba zai ji muryar Allah ko ya bi umurninSa ba. Wannan gaba za ta ci gaba ne tun daga farawa har sai ranar da ubangiji Yesu zai dawo domin ya kai mu sama inda yake. La’ana wanda Allah Ya dora wa Shaidan, babu abin da zai janye shi, hukuncin Allah ya riga ya tabbata bisa Shaidan da duk mabiyansa, to da wannan haushin da yake dauke da shi ne, ya ke yaki domin ya samu mutane da yawa da zai tafi tare da su cikin wutar Jahannama inda za su yi ta kuka da cizon yatsa. Shi ne ya sa a cikin Littafin Ruya ta Yohanna 12: 17: maganar Allah tana cewa “Sai dragon (macijin) ya hasala da gaske da macen, ya tafi domin ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suke kiyaye dokokin Allah, suna rike da shaidar Yesu:” Har zuwa yau, Shaidan yana kara sa kwazo ne sosai domin ya ga yadda zai jawo ra’ayin mutane da dama zuwa nasa garken. Haka nan idan muka duba cikin Littafin 1Bitrus 5 : 8 maganar Allah ta ba mu wannan shawara cewa “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro, Magabcinku Shaidan, kamar zaki mai ruri, yana yawo yana neman wanda zai cinye.” Shaidan shi ne magabcinmu, a nan an kwatanta shi da zaki mai ruri, zaki wanda yake neman abin da zai ci. Idan har zaki yana jin yunwa, zai yi ta neman abinci har sai ya samu; haka Shaidan yake, ba ya hutu ko kadan domin ya san abin da yake nema, idan har ba mu yi zaman tsaro ba, Iblis zai kame mu babu shiri, haka zai kai mu har ga hallaka. Zaman tsaro a nan na nufin mu iya tantance abin da zai gamshi Allah da kuma abin da zai Ya yi fushi da mu; mu kuma guji duk abin da ba zai faranta miSa rai ba. Kada mu yi sakaci cikin bauta wa Allah, domin ta wurin kwazo da lura ne za mu iya sanin dabarun Shaidan mu kuma guje su. Idan muka dubi Littafin Afisawa 6 : 12; Maganar Allah ta riga ta bayana mana cewa: “ Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniyya na mugunta cikin sammai.”
A nan, Allah cikin alherinSa Ya sake nuna mana asirin Shaidan da yadda ya tsara mulkinsa, kada mu yi wasa da wannan, Shaidan yana da tsarin mulki wanda yake amfani da shi, shi ya sa a koyaushe iya yin mugunta a wurare daban-daban kuma kamar a lokaci guda yana da sauki. Yana da masu aiki a madadinsa a ko’ina cikin wannan duniya. Za mu yi kokari mu yi bincike a kan tsarin wannan mulki na Shaidan domin mu iya kare kanmu daga hare-haren da zai kawo mana. Mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa tamu Najeriya da duk shugabanninta. Allah Ya cika su da hikimar shugabanci kamar yadda ya kamata. Ubangiji Allah kuma Ya ci gaba da tsare mu daga kowace irin bala’i. Amin.
Makaman Yaki na Kirista (2)
Kamar yadda muka soma koyarwa a kan Makaman Yaki na Kirista, ina so mu ci gaba da gane wadansu abubuwa:Dole ne kowane mai bin Yesu…