Sai mu gode wa Allah Madaukakin Sarki, Mai komai Mai kowa, Allah Wanda Ya fi gaban misaltawa, domin yawan alherinSa zuwa gare mu, cikin alherinSa Ya bar mu a cikin masu rai a yau. Mu gode maSa domin albarka mai yawa da Ya kawo zuwa gare mu.
A yau bisa ga yardarSa, za mu ci gaba da koyarwar da muke kai, a kan makaman yaki na Krista; kashi na goma sha daya.
Garkuwa-Ta-Ban-Gaskiya:
Maganar Allah tana cewa a cikin Littafin Afisawa 6 : 16; “Musamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya, wadda za ku iya bice dukan jefe-jefe masu wuta na mugun da ita.” Garkuwa kuwa dai ga wanda yake bakin daga, abin kariya ne, garkuwa dai makami ne wanda yana iya kare mutun daga kibiyar da aka harbo. Daga wannan wurin da muka yi karatu; mun gane cewa garkuwar mai bin Yesu Kiristi a koyaushe, ban-gaskiya ce. Idan muka lura, kalmar farko a cikin wannan aya ita ce, “Musamman,” wato garkuwa tana da muhimmanci sosai ga kowane mutum da yake bakin daga, muddin ba ka da garkuwa, to magabci zai iya cin nasara a kanka ba da wahala ba ko kadan, haka nan ga kowane mai bin Yesu Kiristi; muddin ba ka rataya garkuwarka ta ban-gaskiya ba, zai zama da sauki sosai ga Shaidan ya iya cin nasara a kanka. Tambaya ta farko ita ce: (a). Mece ce ban-gaskiya? Idan ban-gaskiya tana da muhimmanci sosai a nan, dole mu gane ko mece ce ban-gaskiya, a cikin Littafin Ibraniyawa 11: 1, maganar Allah tana koya mana cewa: “Ban-gaskiya fa ainihin abin da muke begen ta ce, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.” Wannan bayani a dunkule yake, za mu yi kokari mu yi bincike a kan wannan kalma – Ban-gaskiya; domin irin muhimmanchin da take da shi a cikin rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi. Maganar Allah ta koya mana a cikin Littafin Ibraniyawa 11 : 6 cewa: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da ban-gaskiya: gama mai zuwa wurin Allah sai ya ba da gaskiya akwai Shi, kuma Shi Mai sakawa ne ga ga wadanda ke bidarSa.” Babu wani abu da ya fi muhimmanci a rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi kamar sanin cewa Ubangiji Allah Yana jin dadinsa, sanin cewa Ubangijinmu Yesu Kiristi ya gamsu da duk abin da muke yi, hanya daya ce kawai da mutum zai sa Allah Ya gamsu da shi, wannan kuwa ita ce Ban-gaskiya! Duk rayuwarmu a wannan duniya, muna so ne mu ga cewa mun yi abin da Allah Yake so mu yi. Domin wannan za mu iya cewa, ban-gaskiya, yarda ce da duk abin Ubangiji Allah Ya fadi cikin maganarSa kamar yadda take a rubuce; wato mun yarda da kowane alkawarin da Allah Ya yi wa masu binSa, cewa kamar yadda Ya alkawarta, hakan nan zai faru, Allah ba Ya yin alkawarin da ba Ya cikawa; yarda da haka shi ne ban-gaskiya. Mutanen duniya sukan ce, gani ya kori ji; irin wannan magana tana nuna cewa, idan ban gani da idona ba, ba gaskiya ba ne, wannan yana nuna mana shakku, yayin da shakka tana cewa, sai na gani kafin in yarda, ban-gaskiya kuwa tana cewa, na yarda kuma zan gani, duk inda akwai shakka; sai mu sani babu ban-gaskiya a wurin. A cikin Littafin Markus 11 : 20 – 24 maganar Allah tana cewa: “Da safe kuma sa’ar da suke wucewa, suka ga itacen baure ya yi yaushi tun daga saiwoyin. Bitrus, sa’ar da ya tuna ya ce masa, Rabbi, ka duba, itacen bauren nan wanda ka la’anta shi ya yi yaushi. Yesu ya amsa ya ce musu, ku yi Ban-gaskiya ga Allah. Hakika ina ce maku, duk wanda zai ce wa dutsen nan, ka ciru, ka jefu cikin teku; shi kuwa ba ya yi shakka a ransa ba, amma ya ba da gaskiyar abin da yake fadi zai faru, zai samu. Saboda wannan ina ce muku, duk iyakar abin da kuke addu’a kuna roko kuma, ku ba da gaskiya kun rigaya kun karba za ku samu fa.”
Bari in ba da gajeruwar bayani, a wata rana ne Yesu Kiristi yana tafiya tare da al’majiransa, sai ya ga wata bishiyar baure da take da ganye sosai a kanta, sai ya ratsa domin ya ga ko zai samu ’ya’ya domin ya tsinka ya ci, amma babu komai a kai, maganar Allah ta ce a cikin Littafin Markus 11 : 13-14: “Da ya hangi wani itacen baure mai ganyayen daga nesa, ya zo, ko alama ya samu wani abu a gare shi: sa’ar da ya isa wurinsa, ya iske babu komai sai ganyayen, gama ba lokacin baure ba ne. Ya amsa, ya ce masa, kada kowa ya ci ’ya’ya daga wurinka nan gaba har abada.” Abin da faru ke nan da wannan itacen baure, Yesu Kiristi ya yi magana ne kawai. Washegari itace ya bushe har saiwoyin. Ikon da ke akwai cikin fadin abu ba tare da shakka ba yana da girma sosai. Yesu Kiristi ya koya mana cewa mu ma, idan muka iya yin magana kamar yadda shi ya yi, kuma ba mu yi shakka ba a cikin ranmu, za mu samu duk abin da muka roka daga wurin Allah. Akwai abu guda da ya kamata mu lura da shi a kullum. Wato shakka: mene ne shakka? Rashin yarda cikin zuchiyarka cewa wannan abin zai faru kamar yadda na fadi, abu daya da ke tsayayya tsakanin masu bin Yesu Kiristi da yawancin masu binsa in ya zo ga zancen yin amfani da ban-gaskiya ita ce shakka. Shakka za ta iya nunawa a fuskar mutum, amma gaskiyar ita ce, inda shakka take kafa tushe shi ne cikin zuciyar mutum, idan har shakka ta cika zuciyarka, babu abin da za ka roka daga wurin Allah ka samu. A inda muka yi karatu daga Littafin Markus 11 : 23: Yesu Kiristi da kansa yake magana cewa: “Hakika ina ce muku, duk wanda za ya ce wa dutsen nan, ka ciru, ka jefu cikin teku, shi kuwa bai yi shakka a ransa ba, amma ya ba da gaskiya abin da ya fadi zai faru; zai samu.” Ashe Allah Ya yi wa masu bin Sa shiri mai kyau wanda idan mun sa hankali, za mu zama masu cin nasara a koyaushe. Kada mu manta muna magana ne a kan ban-gaskiya wadda ita ce garkuwar masu bin Yesu Kiristi. Ban-gaskiya babbar makami ne ga kowane mai bin Yesu Kiristi musamman ma a lokacin kalubalen da muke ciki a wannan zamani. Shaidan yakan yi amfani da ’ya’yansa domin su cika zuciyar masu bin Yesu Kiristi da tsoro da fargaba, a hakan nan ne ya iya sa zuciyar mutane da yawa su soma shakkar abin da Allah Ya umarta, ko kuwa ya alkawarta, ban-gaskiya dai ita ce mu yarda cewa Allah ba Ya karya, kuma ba zai taba yi ba, duk abin da ya fadi gaskiya ne, yarda da wannan kuwa shi ne ban-gaskiya, shi ya sa babu wani da zai gamshi Allah idan ba tare da ban-gaskiya ba. Wato mu yarda da shi da kuma duk abin da Ya gaya mana. Ubangiji Ya taimake mu duka.
Za mu ci gaba da wannan koyarwa a kan ban-gaskiya mako mai zuwa idan Allah Ya bar mu a cikin masu rai.
Makaman yaki na Kirista (11)
Sai mu gode wa Allah Madaukakin Sarki, Mai komai Mai kowa, Allah Wanda Ya fi gaban misaltawa, domin yawan alherinSa zuwa gare mu, cikin alherinSa…