✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Makabartun Kaduna na zaizayewa

Akwai bukatar gwamnati ta shigo cikin lamarin, don abin ya fi karfin jama’ar unguwa.

Al’ummar Hayin Taro-Taro da ke Makera Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun koka kan yadda zaizayewar kasa ke lalata makabartar unguwar.

A cewarsu, duk shekara lokacin damina ruwan sama da ke bi ta cikin makabartar mai shekara 45 yana lalata kaburbura inda suke ruftawa a wasu lokutan ruwa ya wuce da kasusuwan mutanen da aka binne shekaru masu yawa.

Hakan yana jefa mutanen da ke makwabtaka da makabarta a cikin damuwa saboda yadda kaburburan suke ruftawa.

Binciken Aminiya ya gano cewa mazauna yankin sukan nemi kasa don toshe kaburburar amma zaizayewar kasar sai ci gaba take yi.

Kuma ta gano sun yi kwalbatoci ta hanyar aikin gayya don canja wa ruwan hanya daga cikin makabartar amma abin ya ki ci, ya ki cinyewa.

Malam Muhammadu Na-Abass, daya daga cikin makwabtan makabartar ya shaida wa Aminiya cewa hakika suna cikin damuwa.

“Da farko ba haka wurin yake ba amma ruwa yau ya zo duk ya wawashe kaburbura a nan, yanzu haka ga wata gawar can kana gani. To, ana yin ruwa zai kara yin gaba da ita.

“Da ruwa ya zo, ba mu iya barci saboda hankalinmu a tashe yake mu da ke da gidaje a kusa.

“Muna kira ga gwamnati ta taimaka mana a gyara wannan makabarta da fitar da hanyar ruwan saboda kullum muna cikin zullumi,” inji shi.

Malam Na-Abass ya ce in ba a gyara wurin ba, suna ji suna gani, za su bar wurin domin dole mutane su watse saboda yadda zaizayewar ke ci gaba da fadada.

Shi ma Is’haka Usman wanda a gidansa ya rasa dakuna hudu saboda ruftawar da suka yi, ya ce abin ci gaba yake yi kuma ga shi talakawa ke zaune a unguwar.

“Duk mazauna yankin nan babu mai karfi da zai iya maganace matsalar sai in Allah Ya sa gwamnati ta sa mana hannu a wannan wuri. Muna neman gudunmawar gwamnati.

“Yanzu haka muna cikin dardar saboda zaizayewar ta fara cin gidaje. Kalli can katanga ce amma ta fadi sannan can kusan dakuna hudu ne amma duk sun rufta,” inji shi.

Shi kuwa Rabi’u Taro-Taro ya bayyana irin kokarin da mazauna yankin suka yi ne domin rage karfin ruwan da ke shiga makabartar.

“A irin kokarin da muke yi mun gina kwalbati kusa da ofishin ’yan sanda don karkartar da ruwan daga shiga cikin makabartar. Sannan mun nemi jama’a su daure su rika gina kwalbatoci a kofar gidajensu,” inji shi.

Ya nuna akwai bukatar gwamnati ta shigo cikin lamarin, inda ya ce abin ya fi karfin jama’ar unguwar.

Mai Unguwar Hayin TaroTaro, Malam Haruna Waziri ya ce suna iya kokarinsu wajen rage karfin ruwan da ke shiga cikin makabartar a kokarinsu na dakatar da zaizayewar kasar.

Ya ce akwai mazauna kusa da makabartar da ba su son yin kwalbati domin a cewarsu idan aka yi ruwa zai rika komawa cikin gidajensu.

“Mun yi iya bakin kokarinmu domin har fada muke yi da mutane wai za mu hana ruwa zuwa makabarta amma su masu rai a tura masu ruwan.

“Mukan ce su yi hakuri su suna da rai za su iya gyara duk inda muka tura ruwan amma a ceci makabartar shi ne abin da ya fi a yanzu.

“Sai da muka je muka kai karar irin wadnnan mutane wurin sarki.

“Kwalbati ne kawai za a gina a wurin da zai hana ruwa shiga makabartar tunda akwai hanyoyin da za a iya hana shi shiga makabartar. Amma ba mu da karfin yin wannan aiki,” inji shi.

Ya ce suna tara kudi ne su sayi kasa domin sake like kaburburan da zaizayewar ke shafa a duk shekara.

Shugaban Kungiyar Masu Kula da Kaburbura ta Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Mohammed Bida ya ce suna bukatar taimakon jar kasa da za a yi ciko saboda rage barnar da zaizayewar ke yi a wurin.

Ya ce, baya ga Makabartar Taro-Taro akwai Makabatar Layin Bilya da wadda ke Hayin Danmani da suke ruftawa saboda zaizayewar kasa.

Ya ce suna matukar bukatar taimako daga wurin masu hannu da shuni da kuma gwamnati.

Shugaban Karamar Hukumar Igabi Alhaji Jabir Khamis ya ce duk yankin Makera na fama da matsalar zaizayewar kasa.

A cewarsa, a bara akwai wani ayari da ya zo daga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ya je makabatar ya dauki hotuna.

“A Makabarta a bara na zuba kasa an toshe wasu kaburbura an kuma zuba maganin ciyawa.

“Ko a yanzu aikin da muke son yi a wurin ba za mu iya ba sai an cire ciyawar wurin, saboda kaburburan suna ta hujewa ana toshewa.

“Amma ainihin aikin zaizayewar kasa karamar hukuma ba za ta iya ba, saboda tunda nake a shekara ta biyar ke nan ban taba samun kudin yaki da zaizayewar kasa ba ballantana mu yi amfani da shi wurin magance matsalar,” inji shi.

Ya ce Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar ta kira shi ta ce an tura kudin aikin, amma ana son bayanan yadda za a kashe su ne.

“Na ji dadin abin domin ko mu aka bai wa za mu yi amfani da su wajen ganin an magance matsalar,” inji shi.

Ya ce ya je makabartar da kansa ya kuma sake dauko hotona inda ya tura wa Kwamishinar don ta gane wa idanunta.

Ya ce Karamar Hukumar Igabi ta fi kowace karamar hukumar a jihar yawan jama’a don haka abu ne da karamar hukumar ba za ta iya yi ba kasancewar akwai hukuma mai kula da zaizayar kasa an kuma sanar da hukumar abin da ke faruwa a yankin.

Sai dai shugaban ya tabbatar da cewa za su yi abin da za su iya yi wajen samar da kasa domin sake cike ramukan da suka rufta tare da samar da hanyar ruwa da za ta karkatar da ruwan da ke bi ta cikin makabartar.

Ya ce za su nemi al’ummar unguwar domin tare da su za a yi wannan aiki amma karamar hukumar ce za ta samar da kudaden da za a yi aikin nan ba da dadewa ba.