Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 wanda ya kai Naira Tiriliyan 54.9.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya gabatar da kasafin kuɗin, inda aka duba shi dalla-dalla kafin a amincewa da shi.
- Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas
- An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe
A majalisar wakilai, ’yan majalisa sun yi nazari kan kasafin kuɗin mataki-mataki kafin su amince da shi a ranar Alhamis.
Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ne, ya gabatar da shi a zaman majalisar.
Bayan tattaunawa da kwamitocin majalisar, an kaɗa ƙuri’ar amincewa da kasafin kuɗin ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen.
Sabon kasafin kuɗin ya ƙunshi kuɗaɗen da aka ware wajen doka, biyan bashi, ayyukan gwamnati, da kuma manyan ayyukan raya ƙasa.
A ɓangaren majalisar dattawa, an amince da kasafin kuɗin bayan rahoton da kwamitin kasafin kuɗi ya gabatar, wanda Sanata Solomon Olamilekan Adeola ke jagoranta.
Bayan kammala karanta takardar kasafin kuɗin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta cikakkun bayanai kafin a kaɗa ƙuri’a.
Sanata Opeyemi Bamidele ne, ya gabatar da ƙudirin amincewa da kasafin kuɗin karo na uku, inda Sanata Abba Moro ya mara masa baya.
Bayan amincewa da kasafin kuɗin, gwamnati ta bayyana yadda za a kashe kuɗaɗe a shekarar 2025, inda za a mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziƙi, manyan ayyuka, da walwalar al’umma.